Rikicin APC a Kano: Ganduje na yunkurin hana Jibrin ficewa daga jam’iyyar

Rikicin APC a Kano: Ganduje na yunkurin hana Jibrin ficewa daga jam’iyyar

  • A yanzu haka masu ruwa da tsaki na kokarin ganin sun hana Abdulmumin Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai ficewa daga APC
  • A ranar Asabar, 7 ga watan Mayu ne Jibrin wanda ya kasance shugaban kungiyar kamfen din Tinubu ya sanar da batun barinsa APC
  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya shiga lamarin kuma an kira taron gaggawa domin magance batun

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, na kokarin hana tsohon dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A ranar Asabar ne Jibrin ya ce zai sanar da sabuwar jam’iyyarsa, yana mai cewa ya yi iya bakin kokarinsa ga APC.

Tsohon dan majalisar shine darakta janar na kungiyar kamfen din Bola Tinubu.

Rikicin APC a Kano: Ganduje na yunkurin hana Jibrin ficewa daga jam’iyyar
Rikicin APC a Kano: Ganduje na yunkurin hana Jibrin ficewa daga jam’iyyar Hoto: Abdulmumin Jibrin
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Abdullahi Abbas, Shugaban APC, ya ce Ganduje ya bukaci a magance rikicin da ke tsakanin masu neman wakiltan mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai. The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bukaci sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar da ta gaggauta daukar matakan da suka dace kan rikicin cikin gida da ya taso daga bangarorin masu neman tikitin takarar mazabar Kiru/Bebeji.
"Saboda haka, sakatariyar jam’iyyar ta hada tare da kiran taron masu ruwa da tsaki don tattauna batun.
“An aika takardar gayyata ga dukkanin masu neman takarar kujerar."

Abbas ya ce tuni Abdulmumin Jibrin Kofa ya amsa takardar kuma a shirye yake ya halarci taron, rahoton Premium Times.

Shugaban jam’iyyar ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki su baiwa jam’iyyar hadin kai domin magance matsalolin da ke tsakanin masu takarar.

Jibrin ya wakilci mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai ta takwas. Ya sake lashe zabe a 2019, amma kotu ta kore shi.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

2023: Tinubu ya saka baki a rikicin APC a Kano bayan Jibrin ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar

A gefe guda, babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya saka baki domin magance rikicin siyasa tsakanin Abdulmumin Jibrin da manyan masu ruwa da tsaki a mazabarsa da ke jihar Kano.

A ranar Asabar, 7 ga watan Mayu ne Jibrin ya sanar da hukuncinsa na barin jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya da bai bayyana ba.

Jibrin bai bayar da kowani dalili da ya sanya shi yanke hukuncin barin APC ba, sai dai majiyoyi sun ce hakan na da nasaba da hukuncin hana shi tikitin komawa majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel