2023: Ga dukkan alamu Buhari na goyon bayan zakulo magajinsa a Kudu, Umahi

2023: Ga dukkan alamu Buhari na goyon bayan zakulo magajinsa a Kudu, Umahi

  • Gwamna David Umahi na Ebonyi kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, ya ce Buhari ya nuna alamun ɗan yankin kudu zia goyi baya a 2023
  • Umahi wanda ya karbi bakuncin shugaban ƙasa na tsawon kwana biyu, ya ce kudu maso gabas ba zata bari a yaudare ta ba
  • Ya ce tun farkon matsayar da gwamnonin kudu suka cimma sun sa a ransu yankin gabashi ne bai taɓa ɗanɗana mulki ba

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce alamun motsin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna yana goyon bayan kai takara kudu, sai dai kawunan yan yankin ya rarrabu.

Gwamnan, wanda ya karbi baƙuncin shugaban ƙasan a Ebonyi ranar Jumu'a, ya yi wannan furucin ne yayin fira da Channesl TV a shirin 'Siyasa a Yau.'

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Shugaban ƙasa Buhari a Ebonyi.
2023: Ga dukkan alamu Buhari na goyon bayan zakulo magajinsa a Kudu, Umahi Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Daily trust ta rahoto Umahi ya ce:

"Mun ƙi yarda da wata gaskiya, tsarin karɓa-karɓa bai hana mutane neman takara ba, hakan ta saba faruwa amma babu wani shafin siyasa da ba tsarin karɓa-karɓa a ƙasar nan."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kuma motsin shugaban ƙasa ya karkata sosai wajen kai takarar shugaban ƙasa yankin kudu, amma idan muka ƙi ɗaukar hakan a matsayin adalci da daidaito, sai mu yaudari kan mu."
"Abun nan kamata ya yi a bar shi a buɗe kowa ya nema saboda idan ba tsarin karɓa-karba, baka da ikon cigaba da ɓaɓatun kada ɗan arewa ya fito takara."

Ba zamu yarda a yaudare mu ba - Umahi

Gwamnan ya ƙara da cewa tun farkon lokacin da suka fara kira da a yi adalci wajen kai takara kudu, sun sa a ransu dan kudu maso gabas za'a baiwa.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto, ya nemi a yi bincike

"Ba zamu yarda a yi amfani da mu wajen kawo takara kudu ba kuma a yaudare mu. Bai kamata mu yi fafutuka kan adalci da daidaito ba kuma mu a ƙi mana haka, wannan ne matsayar shugabannin kudu-gabas."
"Ba ina nufin kada ɗan kudu ta yamma ya nema ba, kundin mulki ya ba shi dama, abinda nike nufi gwamnonin kudu sun buƙaci kawo takara yankin, amma bisa adaalci kudu maso gabas ne a zuciyar mu domin su ne ba su taɓa ɗanɗana wa ba."

A wani labarin kuma Wani Minista Buhari da Sanatan APC sun lale miliyan N200m sun sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya karbi Fom din nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa na APC kan kuɗi miliyan N100m.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Sanatan APC kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun , ya bi sahun saura, ya sayi Fom ɗin takara yau Jumu'a.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262