2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
- Tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, Fatima Abdullahi ta siya fom din takarar gwamna na Jihar Nasarawa
- Yanzu haka tana shirye-shirye tsayawa takara don a yi zaben fidda gwanin jihar da Gwamna Abdullahi Sule na da wata daya
- A ofishin jam’iyyar da ke Lafia ranar Juma’a ta bayyana cewa ta yanke shawarar tsayawa takara ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi
Jihar Nasarawa - Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Ta bayyana cewa za ta tallafa wa matasa idan ta lashe zabe
Kamar yadda ta ce:
“Na yi kudirin tsayawa takara ne saboda ganin halin da jiharmu ta ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki don in kawo gyara, in kuma cika burikan iyaye da kakannin mu. Ina matukar son ganin na kawo canji.
“A ‘yan shekarun nan, na samu damar gogewa ta bangarori da dama, hakan ya sa na ga dalilan tsayawa don kawo wa Jihar Nasarawa ci gaba.
“Matasan mu su na ta mutuwa saboda talauci da rashin tsari, don ba a damawa da su a gwamnati. Idan har na samu nasarar lashe zabe, zan tabbatar na zabo wadanda su ka fi cancanta don su taya ni kawo ci gaban jihar.”
Daga karshe, The Punch ta nuna inda ta bukaci jama’a su mara mata baya, ta hanyar zabenta tun daga zaben fidda gwani don ta samu ta lashe zaben gwamnan jihar a 2023.
Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja
A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.
Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.
Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.
Asali: Legit.ng