Rikicin APC a Kano: Kotun Koli zata yanke hukuncin raba gardama tsakanin Ganduje da Shekarau

Rikicin APC a Kano: Kotun Koli zata yanke hukuncin raba gardama tsakanin Ganduje da Shekarau

  • Kotun koli zata bayyana hukuncin ƙarshe kan rikicin APC a Kano tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau gobe Jumu'a
  • Rikici ya ɓarke a APC reshen Kano har ta kai dare wa gida biyu, tsagin masoyan gwamna da tsagin G-7 na Sanata Shekarau
  • Mazauna garin Kano na tsammanin za'a tsaurara tsaro a jihar domin kiyaye abin da ka iya zuwa ya dawo bayan sanin hukuncin

Abuja - A ranar Jumu'a Kotun Ƙoli zata yanke hukunci kan ƙarar da aka gabatar gabanta game da rikicin shugabanci da ya addabi jam'iyyar APC reshen jihar Kano.

Daily Trust ta rahoto cewa jam'iyyar da tsage gida biyu tsakanin tsagin dake goyon bayan gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Ganduje, da tsagin yan G-7 karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Masu shigar da ƙara a Kotun sun haɗa da Musa Chola da wasu mutum 1,319, sai kuma waɗan da ake ƙara da suka haɗa da APC, Gwamna Buni, Sanata John Akpanudoedehe.

Sauran sune; Olayide Adewale Akinremi, Sanata Abba Ali, Dakta Tony Macfoy, Auwalu Abdullahi, Usman Kaita, Adebayo Iyaniwura da kuma hukumar zaɓe ta ƙasa INEC.

Kotun ƙoli zata yanke hukunci Gobe.
Rikicin APC a Kano: Kotun Koli zata yanke hukuncin raba gardama tsakanin Ganduje da Shekarau Hoto: daiytrust.com
Asali: UGC

Masu shigar da ƙarar waɗan da ke tsagin G-7 su suka fara samun nasara a babbar Kotu, amma tun ba'a je ko ina ba Kotun ɗaukaka ƙara ta warware hukuncin ta ba tsagin Ganduje nasara.

Rashin gamsuwa da lamarin ya sanya ɓangaren masu shigar da ƙara suka garzaya Kotun ƙarshe a ƙasar nan suka bukaci ta jingine hukuncin baya.

Sai dai tsagin Gwamna Ganduje na ganin cewa zuwa Kotun koli da suka yi ba wani sabon abu bane idan mutun ya ɗauki matakin haka, kamar yadda Leadership ta ruwaito

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Bayan jin ta bakin kowane ɓangare a ranar 8 ga watan Afrilu, Kwamitin alƙalai 5 da ke jagorantar shari'ar bisa jagorancin Mai Shari'a Mary Peter-Odili, ta ɗage sauraron hukuncin.

Yaushe za'a yanke hukunci?

Daya ɗaga cinkn lauyoyin dake cikin shari'ar ya faɗa wa jaridar cewa Kotu ta kira su da safiyar Alhamis ta shida musu hukunci ya kammalu kuma za'a sanar da shi ranar Jumu'a.

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan samun labarin lokacin yanke hukunci, kowane ɓangare ya fara nuna yaƙinin samun nasara.

Mazauna Kano sun bayyana cewa suna tsammanin a ƙara tsaurara tsaro a jihar domin kauce wa abin da ka iya zuwa ya dawo bayan hukuncin.

A wani labarin kuma Jirgin Ruwa Maƙare da Yan Shagalin Karamar Sallah Ya Kife a Katsina, An Tsamo Gawar Mutum 18

Aƙalla mutum 18 aka zaro duk a mace mafi yawa kananan yara bayan wani Kwalekwale ya yi hatsari a Katsina.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin kama mataimakin Sufetan yan sanda na ƙasa da SP

Wani shaida ya bayyana cewa Jirgin ya ɗakko mutum 24, har yanzun ana neman ragowar mutum 6 a raye ko a mace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel