2023: Ba Jonathan Bane Ɗan Takarar Da Ya Fi Cancanta Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, Atedo Peterside

2023: Ba Jonathan Bane Ɗan Takarar Da Ya Fi Cancanta Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, Atedo Peterside

  • Wani dan kasuwa kuma masanin tattalin arziki, Atedo Peterside, a ranar Alhamis ya ce jam’iyyun da ke tunanin tsayar da Goodluck Jonathan a matsayin dan takara za su iya shan kaye
  • Ya yi wannan maganar ne yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin din Channels akan batun jam’iyyar APC ta tsayar da Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023
  • A cewar Peterside, duk da dai a 2011 ya zabi Jonathan amma manuniya ta na nuna cewa yanzu haka Jonathan ba zai kai labari ba ko da kuwa an tsayar da shi takarar kasancewar bukatun Najeriya sun karu

A ranar Alhamis, Atedo Peterside, wani dan kasuwa a Najeriya kuma masanin tattalin arziki ya ce jam’iyyun da ke tunanin tsayar da Goodluck Jonathan ba za su samu kuru’u masu yawa ba, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Ya bayyana hakan ne yayin da gidan talabijin din Channels na Sunrise Daily ta tattauna da shi akan jita-jitar komawar tsohon shugaban kasar jam’iyyar APC don tsayawa takara a zaben 2023.

2023: Ba Jonathan Bane Ɗan Takarar Da Ya Fi Cancanta Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, Atedo Peterside
2023: Ba Jonathan Bane Ɗan Takarar Da Ya Fi Cancanta Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa, In Ji Atedo Peterside. Hoto: The Punch.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Peterside, ya zabi Jonathan a 2011, amma manuniya ta nuna cewa yiwuwar nasararsa ta yi kasa kuma ayyukan da ake bukatar shugaban kasar Najeriya ya yi sun karu.

Ya bayyana abubuwan da manuniya ta nuna

A cewar Peterside:

“Kun san ni mutum ne mai daukar kiyasi, amma ayi hakuri, ba zan iya sauya kaina ba. Ina cikin tawagar masu kula da fannin tattalin arziki a lokacin mulkinsa. Kuma na yi aiki a lokacin Yar’Adua.
“Bari in yi amfani da kiyasi, na ce a 2011, akwai yiwuwar Goodluck Jonathan ya lashe zabe kaso 54% amma zuwa lokacin zaben 2015, ya yi kasa ya koma 26%. Sabon kiyasin da manuniya ta nuna shi ne ya kara kasa inda ya koma 5%.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

“Don haka kowa zai iya runtse idonsa akan kiyasin kuma ya fito ya yi abinda ya ke son yi. Ina fatan APC za ta yi kuskuren tsayar da wanda alamun nasararsa su ka yi kasa. Ba za ka iya wasa da hankalin gaba daya mutane ba a lokaci guda.”

Ya bayyana dalilin da ya sa Jonathan ba zai kai labari ba

Ya ci gaba da cewa a shekarar 2011 shi ne dan takarar da ya fi cancanta, amma wannan zamanin ya wuce. Idan ka kalli matsaloli da bukatun da kasa ta ke da su a yanzu, aikin da zai yi a lokacin da kuma yanzu su na da bambanci.

Ya ce zamani ba ya jiran kowa. A cewarsa ba zai ce komai ba dangane da PDP, saboda ya koma SDP a cikin wannan makon.

Ya ce a bangaren jiharsa kuwa mace ce shugaban jam’iyyarsu kuma ko shekaru 35 ba ta kai ba. Matasa ne yanzu su ka fito ba sa son APC, ba sa bukatar PDP, kuma su zai bi, in ji Peterside.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164