An Kwashi Ƴan Kallo Bayan Sanata Mai Neman Takara Ya Fashe Da Kuka a Gaban Mutanen Yankinsa
- A ranar Laraba aka kwashi ‘yan kallo bayan wani sanata mai wakiltar Legas ta yamma, Solomon Olamilekan Adeola ya rushe da kuka gaban jama’ansa
- Kukan ya kwace mishi ne bayan an gabatar masa da fom din tsayawa takara na jam’iyyar APC don ya nemi kujerar sanatan Ogun ta Yamma
- Adeola ya mayar da ‘yancinsa na zabe daga Jihar Legas zuwa Ogun don cika burinsa na tsayawa takarar Sanata na Ogun ta Yamma, inda masoya su ka je har kauyensu don kai masa fom din da su ka siya masa
Ogun - A ranar Laraba aka kwashi ‘yan kallo bayan Sanatan Legas ta Yamma, Solomon Olamilekan Adeola ya rushe da kuka bayan mutane sun kawo masa fom din tsayawa takarar Sanata na Ogun ta Yamma na jam’iyyar APC, Daily Trust ta ruwaito.
Adeola, wanda aka fi sani da Yayi, ya sauya ‘yancin zabensa da kuma kasancewarsa mamban APC daga Legas zuwa Jihar Ogun duk don cimma burinsa na tsayawa takarar Sanata a Ogun ta Yamma.
Sai dai a ranar Laraba shugabannin APC daga Yewa karkashin kungiyar West to West for Dapo Abiodun (W2W4DA) sun kai masa fom din takara na Sanatan Legas ta yamma har kauyensu, Ilaro.
Mutane 71 ne su ka hada kudin fom din cikin kwana biyu
Naija Dailies ta nuna yadda Cheif Mufutau Ajibola, mamban Kungiyar Dattawan Gwamnoni ya gabatar masa da fom din a maimakon daukacin mambobin kungiyar wadanda su ka hada kudi wurin siya masa.
A cewar Ajibola, cikin kwana biyu mutane 71 su ka tara kudin fom din.
A cewarsa, yawancinsu ma’aikatan gwamnati ne, masu ayyuka a kamfanoni ko cibiyoyi masu zaman kansu, ‘yan kasuwa, shugabannin almumma da kuma asalin ‘yan yankin Ogun ta Yamma.
Kamar yadda ya bayyana:
“Gaba daya mutane 71 ne a Ogun ta Yamma, su ka hada kudin cikin sa’o’i 48, tsakanin karfe 3 na yanmacin ranar Litinin, 18 ga wata zuwa ranar Laraba, 20 ga wata.”
“Kamar yadda akwai matasa masu shekaru 30 cikin wadanda su ka hada kudin, akwai tsofaffi masu shekaru 80 da doriya da su ka hada kudin. Kuma an yi wannan ne don taimako da kuma kara dankon zumunci a mazabar Ogun ta Yamma.”
Sanatan ya fara zubar da hawaye saboda murna tare da tuna irin kalubalen da ya fuskanta bayan ya dawo gida ya na neman tikitin tsayawa takara na jam’iyyar.
Ya nuna matukar farin cikinsa
Kamar yadda Adeola ya ce:
“Na gode wa Ubangiji da ya nuna min wannan ranar. Ban san me zan ce ba. Yau ina matukar farin ciki kuma ina godiya ga Ubangiji da mutane na da su ka yi wannan kokarin wurin siya min fom din tsayawa takarar Sanata na Ogun ta yamma.
“Ba zan taba mantawa ba, lokacin da na yanke shawarar dawowa gida na wahala. Ina ta tunanin anya daidai ne matakin da na dauka? Amma sai na ce ni dan Yewa ne haka nan zan dawo."
Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra
A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.
Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.
Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.
Asali: Legit.ng