Kungiyoyi 179 sun ba Zulum kyautar Naira miliyan 50 domin ya saye fam saboda ya zarce

Kungiyoyi 179 sun ba Zulum kyautar Naira miliyan 50 domin ya saye fam saboda ya zarce

  • An samu wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka tarawa Babagana Umara Zulum kyautar N50m
  • Wadannan kungiyoyi sun ba Gwamnan gudumuwa ne saboda jin dadin aikin da ya ke yi a jihar Borno
  • Kungiyoyin su na so Farfesa Zulum ya zarce, ya karbi rokonsu tare da alkawarin cigaba da yin kokari

Borno - Kungiyoyi fiye da 179 su ka hadu su ka tara makudan kudi domin ganin Farfesa Babagana Umara Zulum ya nemi tazarce a kujerar gwamna a jihar Borno.

Mai girma Babagana Umara Zulum ne ya bayyana wannan a shafinsa na Facebook da Twitter.

A ranar Larabar nan ne Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce kungiyoyin sun tara kudi, a karshe su ka gabatar masa da takardar cire Naira miliyan 50 a banki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Mai magana da yawun bakin gamayyar kungiyoyin, Alhaji Awaji Bukar ya ce sun rika tara gudumuwa daga hannun jama’a har da mai bada N1, 000 kacal.

Burin wadannan mutane su ba Gwamnan gudumuwar kudin da zai yanki fam a jam’iyyar APC saboda ganin ayyukan da Gwamnatin Zulum tayi a shekaru uku.

Awaji Bukar ya ce daga 2019 zuwa yau, Gwamna Zulum ya kawo ayyukan more rayuwa fiye da 600 a Borno, ya fito da tsare-tsaren da suka taimakawa 'yan IDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ba Zulum kyautar N50m Hoto: @govborno
An ba Gwamna Babagana Zulum kyautar N50m Hoto: @govborno
Asali: Facebook

A shekaru uku da suka wuce, sama da mutane 10, 000 da ke gudun hijira aka ginawa gidajen zama.

Gwamna Zulum ya yaba

Sanarwar ta ce Zulum ya karbi wannan abin alheri da aka yi masa, ya kuma yabi masu kananan karfin da su ka rika bada gudumuwar da ba ta wuce N1000 ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

A jawabin da ya gabatar, Mai girma Zulum ya sha alwashi ba zai ba marada kunya ba, ya ce zai dage wajen gina tituna, inganta ilmi da kawo ayyukan yi.

Har ila yau, Gwamnan ya ce tun da an fara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, zai maida hankalinsa wajen ginawa al’umma abubuwan more rayuwa.

Shugaban APC ya ji dadi

Shugaban APC na jihar Borno, Ali Bukar Dalori ya yi jawabi a wajen wannan taro da aka yi.

Ali Bukar Dalori ya yabi kungiyoyin da suka ba gwamnan kudin sayen fam, ya ji dadin yadda suke goyon bayan gwamnatin da jam’iyyar APC ta ke jagoranta.

PDP za ta kara da APC a Borno

Kwanakin baya ku ka ji labari cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta samu Naira miliyan 42 daga hannun Alhaji Muhammed Imam da Muhammed Ali a Borno.

Wadannan ‘yan siyasa biyu sun saye fam da nufin neman takarar Gwamnan Borno. Da alama duk wanda ya yi nasara a cikinsu zai yi takara da Babagana Zulum.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Asali: Legit.ng

Online view pixel