2023: Harbe-harben bindiga ya nemi ya birkita taron ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a sakatariya

2023: Harbe-harben bindiga ya nemi ya birkita taron ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a sakatariya

  • Mutane sun ga ta kansu yayin da ‘yan bindiga su ka rika barin wuta a babban birnin jihar Ebonyi
  • Wasu miyagu ne su ka rika harbe-harbe a kan hanyar Enugu zuwa Ebonyi alhali ana bikin sallah
  • Saura watanni suka rage a fara zaben 2023, amma ana fuskantar matsalar rashin tsaro a Najeriya

Ebonyi - An shiga wani halin tashin hankali a sakatariyar jam’iyyar PDP a garin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a ranar Talatar da ta wuce.

Vanguard ta kawo rahoto cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ta barin wuta a gefen hanyar Enugu-Abakaliki, babban titin nan da mutane su ke yawan bi.

‘Ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP sun taru a sakatariyar kenan da nufin za su fara taro, sai aka ji harbe-harben bindigogi sun barke ta ko ina a yankin.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Hakan ya sa mutane suka shiga halin La-hau-la, ‘yan siyasa su ka yi ta neman inda za su ruga su boye yayin da ake hangen miyagun su na barin wuta.

Rahoton ya nuna cewa jama’a sun taru a ofishin jam’iyyar ta PDP ne domin ayi rabon wasu kaya.

‘Yan jarida da suka halarci sakatariyar PDP domin daukar rahoton rabon kayan sun ga ta kansu, domin har da su aka yi carko-carko da aka fara harbin.

'Yan jam’iyyar PDP a sakatariya
Taron PDP a Edo Hoto: www.alamy.com
Asali: UGC

Sai da jami’an tsaro da kuma wasu manyan ‘yan siyasa na jihar Ebonyi su ka kawo agaji, sannan aka iya shan karfin wadannan miyagun ‘yan bindiga.

Har zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoton a yau, Legit.ng Hausa ba ta san dalilin da ya sa ‘yan bindigan su ka yi ta faman wannan harbe-harben ba.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Haka zalika babu adadin wadanda ake tunanin sun jikkata ko sun samu rauni a sanadiyyar harin.

Matsalar tsaro a Najeriya

Yankin kudu maso gabashin Najeriya na cikin inda ake fama da matsalar tsaro a sakamakon aika-aikan haramtaciyyar kungiyar IPOB da sauran tsageru.

Baya ga tsageru da suka fitina yankin, ganin zaben 2023 ya karaso, akwai yiwuwar a rika fuskantar irin wannan barazana har a sauran jihohin kasar.

Obasanjo ya nemi a komawa Na Allah

Ana da labari 'yan kungiyar nan ta Deeper Life Bible Church sun shirya wani taro domin yin addu’o’i a jihar Ogun kuma Olusegun Obasanjo ya samu halarta.

Tsohon shugaban Najeriyar ya ce a halin da ake ciki, akwai bukatar a samu mutane masu daraja su karbi shugabanci domin ba a taba rasa na kwarai a ban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng