Abin da babba ya hango: Olusegun Obasanjo ya fadi wanda Najeriya ta ke bukata a yau

Abin da babba ya hango: Olusegun Obasanjo ya fadi wanda Najeriya ta ke bukata a yau

  • ‘Yan kungiyar nan ta Deeper Life Bible Church sun shirya wani taro domin yin addu’o’i a jihar Ogun
  • Cif Olusegun Obasanjo ya samu halartar wannan taro, inda ya yi kira na musamman ga al’umma
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya ce akwai bukatar a samu mutane masu daraja su karbi shugabanci

Ogun - A ranar Talata, 3 ga watan Mayu 2022, aka ji Cif Olusegun Obasanjo yana mai sa ran cewa nan gaba abubuwa za su dawo daidai a kasar nan.

Tsohon shugaban na Najeriya ya nuna duk halin da aka shiga, za a samu mafita nan gaba a Najeriya. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto.

Olusegun Obasanjo ya yi wannan jawabi a wajen wani taron addu’a da mabiya cocin Deeper Life Bible Church suka shirya a Aboekuta, da ke jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Obasanjo ya yi kira ga al’ummar Najeriya su yarda da Ubangiji, su sa ran abubuwa za su canza zani, ya ce ba za a cire tsammanin rahamar Allah ba.

Lura da yadda abubuwa su ke tafiya yau a kasar nan da ma fadin Duniya, tsohon shugaban ya ce ya zama wajibi Bayin Allah su komawa Mahallicinsu.

Obasanjo
Cif Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan aka lura da abubuwan da suke faruwa a garuruwanmu, jihohinmu, kasashenmu, yankinmu, nahiyarmu ta Afrika da Duniyarmu, ana bukatar addu’o’i irin wannan.”
“Wasu su na zarginmu Kiristoci da yawan adddini ba tare da jin tsoron Ubangiji ba. Eh, gaskiya ne, haka abin yake ko a lokacin Yesu, amma sai mu cire tsammani? A’a.”
“Ba a taba yin wani lokacin da abubuwa suka tabarbare ba, da mutanen Allah ba su fita dabam ba.” - Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara a 2023, Sheikh Gumi

Ba a rasa mutanen Allah

Kamar yadda Vanguard ta fitar da rahoto, Obasanjo ya bada misalai da Annabi Nuhu da kuma Yusuf da suka rike Ubangiji lokacin da fasikai su ka cika Duniya.

A irin wannan yanayi da ake ciki, tsohon sojan ya ce mutane irin wadancan Bayin Allah na kwarai ake bukata su karbi jagoranci domin su iya kawo gyara.

Albarkacin wadannan nagari da ake da su, Ubangiji zai iya kallo da idon rahama, a samu sauki.

A kai mulki Kudu - Ndume

Dazu aka ji labari Sanata Mohammed Ali Ndume ya na tare da masu cewa a bar mutanen kudu su karbi ragamar shugabanci a 2023 saboda a wanzar da adalci.

Sanatan na kudancin jihar Borno ya ce mutanen Arewa za su fi amfana idan shugabanci ya bar hannunsu kamar yadda su ka ci moriyar mulkin Jonathan.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel