Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC ya kammala shiri, zai nemi kujerar Buhari a zaben 2023

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC ya kammala shiri, zai nemi kujerar Buhari a zaben 2023

  • Adams Oshiomhole zai fito ya nemi tikitin yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC
  • Mista Victor Oshioke ne ya bada wannan sanarwa da yawun bakin tsohon Gwamnan na jihar Edo
  • Masu neman zama shugaban Najeriya a APC su na kara yawa, jam’iyya za ta samu kudi da fam

Abuja - Rahotanni na nuna cewa Adams Oshiomhole zai yi takarar shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Jaridar The Cable ta rahoto Victor Oshioke yana cewa Kwamred Adams Oshiomhole zai tsaya takara da nufin ya samu tikiti a jam’iyyar APC a 2023.

Victor Oshioke ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata, 3 ga watan Mayu 2022.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

A cewar hadimin tsohon gwamnan na Edo, Oshiomhole zai shaidawa Duniyar manufarsa a cibiyar fasaha da al’adu na Cyprian Ekwensi a garin Abuja.

Kamar yadda Oshioke ya sanar da ‘yan jarida a jiya, Kwamred Oshiomhole ya yi niyyar ayyana burinsa tun tuni, amma sai aka ba shi shawarar ya dakata.

“An canza ranar fitowa ayyana takarar kujerar shugaban kasa da Kwamred Adams Aliyu Oshiomhole zai yi na zaben 2023.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adams Oshiomhole
Tsohon Shugaban APC, Adams Oshiomhole Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Depositphotos
“Hakan ya na zuwa ne bayan daga lokacin da aka sa tun farko, a sakamakon dogon zama da tattaunawa da Oshiomhole ya rika yi.”
“Mu na bada hakurin fitar da sanarwar a tsuke, tare da fatan kaunar da ku ke yi wa Adams Oshiomhole zai isa ku halarta duk runtsi.”

Ina batun neman Sanata?

Jaridar ta ce wannan sanarwa na zuwa ne makonni kadan bayan samun labarin cewa Oshiomhole zai nemi kujerar Sanatan Edo ta Arewa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Sanata Francis Alimikhena mai wakiltar mazabar Arewacin jihar Edo ya sake sayen fam. Alamu na nuna cewa akwai yiwuwar Sanatan ya zarce a 2023.

Tikitin APC sai mai rabo

Hakan ya sa masu sha’awar kujerar shugaban kasa a APC yankin kudu maso kudancin Najeriya suka karu, baya ga Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio.

A hutun idin nan ne labari ya zo mana cewa Sanata Godswill Akpabio zai shaidawa Duniya nufinsa na zama shugaban Najeiya a zaben da za ayi a 2023.

Idan abubuwa sun tafi daidai, tsohon gwamnan na Akwa Ibom zai saye fam a ranar Larabar nan. Akpabio yana cikin 'yan siyasan da ake ji da su a Neja Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng