Wani Ministan Buhari zai ayyana shirin takarar Shugaban kasa nan da awanni 48

Wani Ministan Buhari zai ayyana shirin takarar Shugaban kasa nan da awanni 48

  • Sanata Godswill Akpabio zai shaidawa Duniya nufinsa na zama shugaban Najeiya a zaben 2023
  • Idan abubuwa sun tafi daidai, tsohon gwamnan na Akwa Ibom zai saye fam a ranar Larabar nan
  • Akpbaio zai gwabza da Amaechi, Chukwuemeka Nwajiuba da Chris Ngige wajen samun tuta a APC

Abuja - Godswill Akpabio wanda yake rike da kujerar Ministan Neja Delta zai fito takarar shugaban kasa a ranar Laraba, 4 ga watan Mayu 2022.

Anietie Ekong wanda yake magana da yawun bakin Sanata Godswill Akpabio ya shaidawa manema labarai wannan. The Cable ta fitar da rahoton.

Da aka zanta da Hadimin Ministan a ranar Litinin, ya tabbatar da cewa mai gidansa zai yi takara.

Kamar yadda Ekong ya shaidawa ‘yan jarida, labarin da ke yawo a game da takarar Ministan ba karya ba ne, zai ayyana takararsa a tsakiyar makon nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

“Eh, gaskiya ne. Zai bayyana shirin takara a ranar Laraba.” - Anietie Ekong

Ministoci za su nemi mulki

Hakan yana nufin Ministan harkokin na Neja-Deltan shi ne Minista na hudu a gwamnatin Muhammadu Buhari da ke hangen kujerar shugaban kasa.

Legit.ng ta na da labari cewa bayan Sanata Akpabio, akwai Rotimi Amaechi, Chris Ngige da Chukwuemeka Nwajiuba da za su nemi tikitin APC a 2023.

Wani Ministan Buhari
Akpabio, Lai da Ita Enang Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shiga takarar Ministocin ya jawo surutu ganin a yanzu haka kungiyar malaman jami’a na yajin-aiki, sannan an daina amfani da jirgin kasan Kaduna-Abuja.

A wani rahoton, an ji Akpabio zai saye fam ne a ranar Alhamis, saurana kwana daya a rufe saida fam.

Nan da ranar 28 ga watan Mayu ake sa rai APC mai mulki za ta tsaida ‘dan takararta. A lokacin ne za a san wanda zai rikewa jam’iyyar tikiti a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC 10 da ka iya maye gurbin ministocin Buhari masu ficewa

Tarihin siyasar Akpabio

Godswill Akpabio ya yi mulki na tsawon shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Akwa Ibom daga 2007 zuwa 2015. Akpabio ya yi mulki ne a jam’iyyar PDP.

Bayan ya kammala wa’adinsa, sai Akpabio ya sama Sanata duk a karkashin PDP. Amma daga baya sai aka ji ya sauya-sheka zuwa APC mai rinjaye a 2018.

Bayan zaben 2019, Sanatan bai iya zarcewa a kan kujerarsa ba, sai aka nada shi Minista.

Takarar Ahmad Lawan

Sauran wadanda Akpabio zai fuskanata a zaben su ne, Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, Yahaya Bello. Sannan ana rade-radin Dr. Ahmad Lawan zai nemi tuta a 2023.

Jita-jita su na cewa a makon nan shugaban majalisar dattawa na kasar nan, Ahmad Ibrahim Lawan zai bayyana nufinsa na neman zama shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel