Ana shirin tunkarar 2023, Sanata Kola Balogan, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP

Ana shirin tunkarar 2023, Sanata Kola Balogan, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP

  • Yayin da kowace jam'iyyar siyasa ke ƙoƙarin dinke ɓarakarta domin tunkarar 2023, PDP ta yi sake Sanata ɗaya tilo daga Oyo ya yi murabus
  • Sanata Kola Balogun, mai wakiltar Oyo ta Kudu ya aike wa PDP wasikar murabus daga kasancewarsa ɗan jam'iyya
  • Balogun wanda ƙani ne ga babban basaraken Ibadan ya gode wa tsohuwar jam'iyyarsa a wasikar da ya rubuta

Oyo- Sanata Kola Balogun mai wakiltar mazaɓar jihar Oyo ta kudu, ya tabbatar da yin murabus daga kasancewarsa mamba a jam'iyyar People Democratic Party (PDP).

Wannan matakin na ƙunshe a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin Midiya, Dapo Falade, ya fitar ranar Litinin da yamma a Ibadan, kamar yadda Punch ta ruwaito.

NAN ta rahoto cewa Sanatan, wanda ɗan uwa ne ga Olubadan na Ibadan, Oba Lekan Balogun, shi ne mataimakin shugaban kwamitin wasanni da cigaban matasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Sanata Kola Balogun.
Ana shirin tunkarar 2023, Sanata Kola Balogan, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ficewar sanatan daga jam'iyyar ya zo ne kwanaki kaɗan bayan PDP ta tabbatar ba zata ba shi tikicin tazarce ba a zaben 2023.

Bayanai sun nuna cewa PDP ta baiwa Chief Joseph Tegbe, tikicin duk da bai jima da sauya sheƙa daga APC zuwa PDP ba.

A wasikar da ya aike wa shugaban PDP na gunduma ta 12 a Ibadan Arewa-Gabas, Tijani Wasiu, ya gode wa jam'iyya bisa damar da ta ba shi na shiga majalisa ta tara, ya sanar cewa murabus ɗinsa zai fara aiki daga 28 ga watan Afrilu.

Balogun ya ce ya ji daɗin haɗin kan da shugabannin PDP da mambobi suka ba shi tun farko har zuwa watan Afrilu, inda ya yi wa jam'iyya fatan Alkairi.

Premium Times ta rahoto Ya ce:

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

"Ni, Sanata Kola Balogun mai wakiltar mazaɓar Oyo ta kudu a majalisar dattawa ta 9, na yi murabus daga jam'iyyar PDP daga ranar 28 ga watan Afrilu."
"Ina ganin PDP ce ta bani dama har na wakilci mutanen mazaɓata a majalisar tarayyan Najeriya kuma na ji daɗin haɗin kan da ta bani har zuwa lokacin murabus ɗina."

Wasu mambobin PDP da ADC sun koma APC a Oyo

Sanata Balogun ne kaɗai Sanatan PDP daga jihar Oyo a majalisa ta Tara har zuwa lokacin da ya fice daga jam'iyyar.

Sai dai matakin fita daga PDP da sanatan ya ɗauka ya zo ne awanni 48 bayan wasu dandazon mambobin PDP, da ADC sun koma jam'iyyar APC a jihar.

A wani labarin na daban kuma Daga ƙarshe, Shugaba Buhari ya faɗi mutumin da zai miƙa wa mulkin Najeriya a 2023

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ƙara magana kan wanda zai iya miƙa wa ragamar mulkin Najeriya bayan zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Da aka tambaye shi kan haka bayan kammala Sallar Idi a Abuja, Buhari yace zai miƙa mulki ga duk wanda yan Najeriya suka zaɓa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel