Shugaba a 2023: ‘Yan takarar APC sun shiga rudani yayin da Buhari ya goyi bayan kowannensu

Shugaba a 2023: ‘Yan takarar APC sun shiga rudani yayin da Buhari ya goyi bayan kowannensu

  • Rahotanni sun kawo cewa akwai rudani a tsakanin masu shugabancin kasa na APC kan wanda zai zama dan takarar jam’iyyar a cikinsu
  • Yawancinsu suna lalube ne a cikin duhu tare da rashin tabass kan wanda Shugaba Buhari zai marawa baya a cikinsu
  • An dai tattaro cewa shugaban kasar ya nuna goyon bayan dukkanin masu neman shugabancin kasar da suka ziyarce shi don fada masa kudirinsu

Yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na cikin rudani da fargaba a yanzu haka kan salon da za a bi wajen zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar bayan zaben fidda gwani.

Wani jigon jam’iyyar ya fada ma jaridar The Sun cewa adadin masu neman takarar ya karu ne saboda ganin cewa shugaban kasa mai ci ya kammala cikakkiyar wa’adin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Shugaba a 2023: ‘Yan takarar APC sun shiga rudani yayin da Buhari ya goyi bayan kowannensu
Shugaba a 2023: ‘Yan takarar APC sun shiga rudani yayin da Buhari ya goyi bayan kowannensu Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Akalla jiga-jigan APC guda 10 ne suka nuna sha’awarsu wajen son mallakar tikitin jam’iyya mai mulki.

Duk da cewar yan takarar sun ayyana kudirinsu harma wasun su sun siya tikitin neman takara na naira miliyan 100, da dama daga cikinsu na lalube ne a cikin duhu da rashin tabbass kan yadda za a zabi wanda zai rike tutar jam’iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Domin karrama shi, kusan dukka yan takarar sun tunkari shugaban kasa Muhammadu Buhari domin sanar da shi kudirinsu kafin su sanar da duniya, amma abun mamaki dukkaninsu sun samu goyon bayan shi.

Yan takarar sun shiga halin rashin tabbass tun bayan da shugaba Buhari ya bayyana cewa za a kashe dan takarar da yake goyon baya idan ya bayyana sunansa.

Sai dai, a kokarinsu na sanyayawa yan takarar gwiwa, shugabancin jam’iyyar ya tsawwala kudin fom din takarar shugaban kasa har zuwa naira miliyan 100.

Kara karanta wannan

Wani dan takarar shugaban kasa ya karaya ya kai karar PDP kan kudin fom N40m

Sai dai kuma, duk da siyar fom din da suka yi da tsada, yan takarar sun shiga rudani bayan shugaban kasa Buhari ya goyi bayan kusa dukkan su.

A cewar majiyoyi, akwai yiwuwar a kara maimaita abun da ya faru a yayin babban taron jam’iyyar na kasa lokacin da Buhari ya goyi bayan Sanata Abdullahi Adamu sannan hakan ya tsorata sauran yan takara har suka janye daga tseren.

Yayin da suke fama da rashin tabbass, yan takarar da ke kokarin yiwa junansu wayo, suna ta ci gaba da amfani da sunan shugaban kasa yayin da kowanne ke nuna kamar shine zabinsa.

Da yake magana a kan damar da yan takarar shugaban kasa ke da shi, wani mamba a kwamitin NWC ya fada ma jaridar The Sun cewa abu ne mai wahala kamar yadda aka saba, yana mai cewa kusan ba zai taba yiwuwa wani dan jam’iyyar ya fito fili ya fadi yadda dan takarar jam’iyyar zai bayyana ba.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka saboda dalilai

Jigon jam'iyyar ya ce:

“Duk wanda ya fada maka cewa ya san ta yadda za a zabi dan takarar jam’iyyar toh dole yana da kamshin gaskiya. Bisa ga dukkan alamu, abun zai kasance na kudu ne saboda baya ga Gwamna Yahaya Bello wanda ya fito daga arewa ta tsakiya, babu wani dan takara da ya fito daga arewa.
“Kusan a bayyane yake cewa dan takarar shugaban kasa ba zai fito ta tsarin da aka saba na zaben fidda gwani ba saboda jam’iyyar na son rage fafatawa a zaben fidda gwani.
“Sai dai, zan iya fada maku cewa akwai fargaba da tsoro a zukatan masu takara saboda sun yanke shawarar cewa shugaba Buhari ne zai zabi wanda zai daga tutar jam’iyyar.
“Abun da ke zukatan yan takara shine cewa shugaban kasa zai yi amfani da tsarin da yay i amfani da shi a babban taron jam’iyyar wajen daura dan takarar da ya fi soyuwa a zuciyarsa.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

A gefe guda, ministan sufuri kuma, Rotimi Amaechi ya jadadda biyayyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin da yake shirin neman shugabancin kasar a 2023.

Wata sanarwa daga ofishin labaransa ya ce Amaechi ya magantu ne a lokacin wata ganawa da shugabanni, wakilai da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar APC ta jihar Ribas a ranar Juma’a, Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana cewa a yunkurinsa na son zama shugaban kasar Najeriya wanda ya cancanci hawa kujerar, bai kasance mai gaggawa ko rashin biyayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng