Abin Da Yasa Ƴan Siyasa Ke Ɗaukan Alkawurran Da Ba Za Su Iya Cika Wa Ba, Ɗan Majalisar Najeriya

Abin Da Yasa Ƴan Siyasa Ke Ɗaukan Alkawurran Da Ba Za Su Iya Cika Wa Ba, Ɗan Majalisar Najeriya

  • Mr Dachung Bagos, dan majalisar dokokin tarayya ya ce yan siyasa su kan dauki alkawurran da ba za su iya cika wa ba kawai don su ci zabe
  • Dan Majalisar mai wakiltar Jos South/Jos East ta Jihar Plateau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels Television
  • Bagos ya kuma roki yan Najeriya su rika yi musu adalci don a cewarsa babu yadda mutum 500 za su warware matsalolin mutane fiye da miliyan 200

Mutane da dama masu rike da mukamai suna yin alkawurran da ba za su iya cika wa ba yayin yakin neman zabe saboda kawai suna son su ci zabe, a cewar wani dan majalisa a ranar Asabar.

Mr Dachung Bagos, dan majalisar dokokin tarayya, ne ya yi wannan bayanin yayin tattaunawa da aka yi da shi kan ayyukan yan majalisa a mazabunsu.

Kara karanta wannan

Za a Sha Jar Miya: Zan Naɗa Ministan 'Raya Ƙunɗu' Idan Aka Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, In Ji Fayose

Abin Da Yasa Ƴan Siyasa Ke Ɗaukan Alkawurran Da Ba Za Su Iya Cika Wa Ba, Ɗan Majalisar Najeriya
Yan Siyasa Na Yin Alkawurran Da Ba Za Su Iya Cika Wa Ba Don Su Samu Kuri'a, Dan Majalisar Tarayya. Hoto: Channels Television.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bagos, wanda ke wakiltar Jos South/Jos East ta Jihar Plateau ya yi wannan jawabin ne yayin shiri na musamman - Open Square da aka nuna a Channels Television.

"Za ka tsinci kanka kana yin alkawurra yayin kamfen amma saboda yan siyasa ne neman kuri'u, sai suyi ta cewa eh eh," in ji shi.
"Yanayin siyasar Najeriya ta saka yan siyasa suna yin alkawurra fiye da kima, idan kuma ka yi hakan, za ka ga abubuwa sun maka yawa.
"Akwai abubuwan da zaka fada lokacin kamfen, kuma za a tuna maka; za a nuna maka bidiyon kamfen din ka."

Dan majalisar ya ce yana son yan Najeriya su rika yi wa yan majalisa adalci, yana mai cewa yan majalisar suna yin ayyukansu yadda ya kamata, rahoton FGN News.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

A cewarsa, ba daidai bane a yi tsammanin mutanen ba su kai 500 ba za su warware matsalolin kasa da ke da al'umma fiye da miliyan 200.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Da Ke Son Gadon Kujerar Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka Adabi Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel