Za a Sha Jar Miya: Zan Naɗa Ministan 'Raya Ƙunɗu' Idan Aka Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, In Ji Fayose

Za a Sha Jar Miya: Zan Naɗa Ministan 'Raya Ƙunɗu' Idan Aka Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, In Ji Fayose

  • Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma dan takarar shugaban kasa a PDP ya yi alkawarin nada ministan Raya Kundu idan ya ci zabe
  • Fayose ya furta hakan ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin tantance yan takarar jam'iyyar PDP a ranar Juma'a
  • Ya ce gina tituna da sauran ayyukan more rayuwa suna da muhimmanci amma al'umma ba za su more su ba idan suna fama da yunwa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya yi magana a gaban kwamitin tantance yan takarar jam'iyyar PDP inda ya yi alkawarin zai nada ministan 'raya kundu' idan aka zabe shi shugaban kasa, rahoton The Cable.

Fayose ya ce a lokacin da mambobin kwamitin suka masa tambaya game da tsarinsa na raya kundu yayin da ya ke gwamna a Jihar Ekiti, ya fayyace musu cewa zai cigaba da tsarin idan ya zama shugaban kasa kamar yadda ita ma Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Sanatan APC Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023

Za a Sha Jar Miya: Zan Naɗa Ministan 'Raya Kunɗu' Idan Aka Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa, In Ji Fayose
Fayose Ga 'Yan Najeriya: Zan Naɗa Ministan 'Raya Kunɗu' Idan Aka Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa.
Asali: Twitter

"Na fada musu karara cewa zan nada ministan raya kundu da walwalar al'umma," a cewar Fayose.

Gine-ginen tituna da wasu ayyukan more rayuwa suna da kyau amma dole sai mutane sun koshi za su more su, In ji Fayose

Ya ce, duk da cewa shimfida tituna da kwalta da wasu ayyukan gine-gine suna da muhimmanci, ba za su yi tasiri ba idan mutane suna fama da yunwa.

"A bangare na, tsarin raya kundu yana daga cikin hanyoyin tallafawa talakawan Najeriya. Raya Kundu a gwamnati na a matsayin shugaban kasa zai kasance cikin ababe masu muhimmanci.
"Babu wanda ke cewa kada ka yi wasu ayyuka na cigaba da raya kasa, amma kula da walwala da jin dadin al'umma shima yana cikin ayyukan cigaba."

Kara karanta wannan

Tallafin abinci: Gwamnatin Borno ta damke mutum 26 da ke karbar cin hanci daga IDPs mata

Da ya ke magana kan tsarin karba-karba, Fayose ya ce yana ganin ya dace PDP ta cigaba da tsarin domin kada a kawo rudani.

A cewarsa, ko da jam'iyyar na son kowa ya yi takara, ta bayyana a hukumance cewa yankin kudu za ta bawa tikitin takarar.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel