Sallah: Tinubu ya gwangwaje Musulmai da buhunan shinkafa 3,000 a Nasarawa
- Ana tsaka da shirye-shiryen shagalin bikin sallah, Bola Tinubu ya bada kyautar buhunan shinkafa 3,000 ga musulman kwarai a jihar Nasarawa
- Yayi hakan ne don taimakawa marasa karfi wajen yin shagalin bikin sallah cikin farinciki, bayan dubi da tsadar rayuwar da ake ciki
- Haka zalika, ya nemi goyon bayan mambobin jam'iyyar APC da dukkan'yan Najeriya wajen ganin mafarkinsa na zama shugaban kasa ya zama gaskiya
Nasarawa - Yayin da shirin bikin sallah ya karato, tsohon gwamnan Legas, kuma 'dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 karkashin jami'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bada kyautar buhunan shinkafa 3,000 ga musulman kwarai a jihar Nasarawa, rahoto jaridar Punch ya bayyana.
Tinubu, yayin bada kyautar buhunan shinkafan a ranar Juma'a a Lafia, ya bukaci wadanda suka samu tagomashin da kada su siyar da shinkafar, amma su yi amfani da ita a kan dalilin da yasa aka basu, inda ya ce an yi hakan ne don rage tsadar rayuwar da ake ciki.
TVC News ta rahoto cewa, Yusuf Omaku, mai kula da kungiyar kamfen din Bola Ahmed Asiwaju Tinubu na jihar Nasarawa ne ya wakilce shi.
Ya ce, "wannan kyautar an bada ta ne don tallafawa mutane, musamman marasa karfi a jihar Nasarawa, saboda bikin karamar sallar Eidi da ke karatowa.
"Ina so in yi amfani da wannan damar wajen kira ga 'yan Najeriya da su zabi shugabannin da suka dace a zaben da za a yi a shekara mai zuwa, don yin garanbawul ga matsalolin tattalin arzirkin dake kawo cikas ga cigaban kasa.
"Saboda haka ne, nake neman goyon bayan mambobin jam'iyyar APC da dukkan 'yan Najeriya da su mara min baya wajen ganin na cika burina na zama shugaban kasa.
"Buhunan shinkafan guda 3,000 da aka bada ga jihar Nasarawa, za a raba su ga kungiyoyi, wuraren bauta, sanannun kungiyoyi da 'yan jam'iyyar APC mara karfi."
2023: An karba wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya karbi fom din N100m na jam’iyyar APC domin tsayawa takarar shugaban kasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Vanguard ta ruwaito cewa, jiga-jigan kungiyar goyon bayan Tiubu ta TSG ce ta dura cibiyar taron kasa da kasa ICC domin sayen fom din a madadin Tinubu.
An tattaro cewa Tinubu, wanda ya tafi kasar Saudiyya aikin Hajji, ya samu wakilcin wasu makusantan sa da suka hada da dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Ikeja, James Faleke.
Asali: Legit.ng