Ba Za Ku Iya Maguɗin Zaɓe Ba a 2023, Buhari Ya Faɗa Wa 'Yan Siyasa

Ba Za Ku Iya Maguɗin Zaɓe Ba a 2023, Buhari Ya Faɗa Wa 'Yan Siyasa

  • Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin tabbatar da zaben gaskiya da gaskiya a shekarar 2023 don kare kuru’un ‘yan Najeriya
  • Ya yi wannan alkawarin ne a ranar Alhamis yayin liyafar buda-bakin da ya yi da mambobin ofishin jakadanci na kasashe daban-daban
  • Ya shawarci ‘yan siyasar da ke da shirin yin magudin zabe a gagarumin zaben 2023 da ke karatowa da su sauya tunani

Abuja - Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kare kuru’un ‘yan Najeriya ta hanyar tabbatar da an yi zaben-gaskiya da gaskiya a shekarar 2023 da ke karatowa, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis a wata liyafar buda-baki da ya yi da mambobin ofishin jakadanci kasashen waje a Najeriya.

Ba Za Ku Iya Maguɗin Zaɓe Ba a 2023, Buhari Ya Faɗa Wa 'Yan Siyasa
Ba Za Ku Iya Maguɗin Zaɓe Ba a 2023, Buhari Ga 'Yan Siyasa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Ya bai wa ‘yan siyasar da ke da shirin yin magudin zabe a 2023 shawarar su sauya tunani.

Kara karanta wannan

An buga an bar ka: Abin da ya sa aka gagara tsige ni daga shugaban majalisar - Bukola Saraki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Duk masu shirin yin magudin zabe a zaben da ke zuwa su sauya tunani saboda ina da shirin kare kuru’un duk wasu ‘yan Najeriya.”

Buhari ya ja kunnen kasashen ketare daga shiga harkokin zabe mai zuwa.

Buhari ya ce ya jajirce wurin yin ingantaccen zabe

Kamar yadda Nigerian Tribune ta nuna, ya ci gaba da cewa:

“Kamar yadda ku ka sani, zan kammala mulkina a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Kowa ya san yadda al’amuran zabe suke zuwa.
“Haka demokradiyya ta ke. Ina da shirin jajircewa wurin shirya nagartaccen zabe fiye da wanda na tarar.
“Yayin da Najeriya ta ke kokarin wuce wannan siratsin, ina bukatar ku abokanmu na duniya da ku kiyaye shiga harkar zabe ko kuma goyon bayan wasu ‘yan takara.”

Shugaban kasa na barar addu’a daga mutane musamman musulmai don zaman lafiya ya wanzu a kasashe

Kara karanta wannan

Ba na jin tsoron kowa a APC, Yahaya Bello ya karfafi rade-radin takarar Jonathan a 2023

Yayin da Buhari ya ke jawabi dangane da fadan Rasha da Ukraine, ya bukaci a kai tallafi ga wadanda su ke mawuyacin yanayi wadanda yakin ya shafa.

Ya ce in har ba a yi gaggawar samar da maslaha ba, abubuwa za su iya kara kazanta.

Shugaban kasa ya samu tarbar sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Gutteres, inda ya yaba wa kokarinsa na ganin an dakatar da fadace-fadacen.

Shugaban kasa ya bukaci mutanen duniya, musamman musulmai su yi amfani da damar watan Ramadan musamman ranakun karshen watan wurin dagewa wurin addu’ar ganin karshen fadan Rasha da Ukraine don zaman lafiya ya dawo.

Dangane da COVID-19, shugaban kasa ya ce Najeriya za ta ci gaba da samar da magunguna da allurar riga-kafin cutar don kawo karshenta.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel