Zaben 2023: Yau masu harin kujerar Shugaban kasa a PDP za su san matsayin takararsu

Zaben 2023: Yau masu harin kujerar Shugaban kasa a PDP za su san matsayin takararsu

  • Ranar Juma’a, 29 ga watan Afrilu 2022 za a tantance masu neman shugaban kasa a jam’iyyar PDP
  • Wadanda suka saye fam za su bayyana a gaban Sanata David Mark da ‘Yan kwamitinsa a Abuja
  • Atiku Abubakar, Bukola Saraki, da Peter Obi su na cikin masu shirin shiga takarar shugaban kasa

Abuja - ‘Yan siyasa kimanin 17 da suka saye fam din neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP za su bayyana a gaban kwamitin da zai tantance su.

Daily Trust ta ce yau Juma’a, 29 ga watan Afrilu 2022 za a tantance ‘yan takarar a babban ofishin da PDP ta tanada domin yakin neman zaben shugaban kasa.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark yake jagorantar wannan kwamiti na mutum tara da zai tantance masu neman takara.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran PDP ya kai karar Jam’iyya a kotu, ya bukaci a dakatar da zaben tsaida gwani

Jaridar ta ce ragowar ‘yan kwamitin su ne Cif Celestine Omehia; Cif Mike Ahamba (SAN); Dr Olusegun Mimiko; Edward Ashiekaa (SAN), da Hilda Makanto.

David Mark yana cikin manyan ‘yan siyasan Najeriya, ya dade a kan kujerar majalisar dattawa. Shi karon kansa Sanatan ya nemi takarar shugaban kasa a 2019.

Ahamba da Edward Ashiekaa kwararrun lauyoyi ne, Omehia kuma tsohon gwamnan Ribas ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manyan 'Yan PDP
Atiku, Saraki, Tambuwal da Bala Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Sai Dr. Mimiko wanda tsohon gwamna ne wanda ya yi mulki a jihar Ondo a karkashin jam’iyyar hamayya ta Labour Party, daga baya ya shigo jirgin PDP.

Makanto ce macen da ke cikin wannan kwamiti, ta na cikin matasan da ake ji da su a yau.

Masu neman tuta a PDP

Legit.ng Hausa ta na da labarin ‘yan takarar su ne; Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal, Bukola Saraki, Anyim Pius Anyim sai kuma Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Har ila yau akwai Nyesom Wike, Udom Emmanuel, Peter Obi, Ayodele Fayose, Dele Momodu, Mohammed Hayatu-Deen, Cosmos Ndukwe da Charles Ugwu.

A karshe akwai; Sam Ohuabunwa, Chikwendu Kalu, Nwachukwu Anakwenze da Oliver Tareila Diana.

Da zarar an tantance mai neman takara, za a ba shi takardar shaida wanda za ta ba shi damar shiga zaben fitar da gwani wajen neman tikitin jam’iyya a zabe.

Siyasar APC a Kaduna

Dazu aka samu rahoto Asmau Sani Sha’aban da ‘yanuwanta sun hada gudumuwar kudi domin mahaifinsu, Sani Sha'aban ya yi takarar Gwamnan Kaduna.

Sani Muhammed Sha’aban wanda suruki ne wajen shugaban kasa zai fito takara a zaben 2023, ya ci burin darewa kujerar Mal. Nasir El-Rufai a jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng