Yaran tsohon ‘Dan Majalisa sun sayawa mahaifinsu fam domin ya nemi Gwamna a Kaduna

Yaran tsohon ‘Dan Majalisa sun sayawa mahaifinsu fam domin ya nemi Gwamna a Kaduna

  • A jihar Kaduna, ‘ya ‘yan Sani Muhammed Sha’aban ne suka hada miliyoyi domin saya masa fam
  • An biya N50m domin sayawa tsohon ‘dan majalisar fam din shiga zaben gwamna a jam’iyyar APC
  • Yaran Hon. Muhammed Sha’aban su na ganin shi ne wanda ya dace ya gaji Gwamna Nasir El-Rufai

Kaduna - A ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu 2022, ‘ya ‘yan da Sani Muhammed Sha’aban da ya haifa su ka saya masa fam domin ya shiga takarar gwamna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto ‘ya ‘yan Hon. Sani Muhammed Sha’aban su na cewa su suka hada gudumuwar N50m da aka saya masa fam na shiga takara a APC.

Asmau Sani Sha’aban ta ce ita da wasu ‘yanuwanta 16 suka yi karo-karo domin mahaifinsu, tsohon ‘dan majalisar ya nemi kujerar gwamna a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yau masu harin kujerar Shugaban kasa a PDP za su san matsayin takararsu

Kamar yadda Asmau Sani Sha’aban ta shaidawa manema labarai, mahaifinsu zai yi takara ne domin inganta halin da mutanen Kaduna ke ciki a halin yanzu.

Sani Sha’aban ne ya dace

‘Diyar ‘dan siyasar ta ce gwamnatin Malam Nasir El-Rufai mai-ci tayi kokari a jihar Kaduna, amma akwai ragowar aiki wajen kawo cigaban da ake nema.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ra’ayin Asmau Sha’aban, babu wanda ya dace ya zama magajin Malam El-Rufai irin mahaifinsu.

Yaran tsohon ‘Dan Majalisa sun sayawa mahaifinsu fam domin ya nemi Gwamna a Kaduna
Sani Muhammed Sha’aban ya saye fam a APC Hoto: Ahmed Tijjani Ramalan
Asali: Facebook

Sani Muhammed Sha’aban ya na da goyon bayan talakawa, kuma yana tare da manyan kasa, baya ga cewa ya san aiki, sannan zai iya mulkin jihar, a cewar ta.

“Na yi imani cewa yana da abin da ake bukata wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar nan, sannan kuma ya inganta halin tattalin arziki.”

- Asmau Sani Sha’aban

A tsaida nagari a APC - Sha'aban

Kara karanta wannan

An buga an bar ka: Abin da ya sa aka gagara tsige ni daga shugaban majalisar - Bukola Saraki

Legit.ng Hausa ta na da labari cewa Danburam din na Zazzau kuma Barden Keffi yana cigaba da kokarin ganin shi ne ya samu tikitin APC a Kaduna a zaben 2023.

Sani Sha’aban ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyya da suke zaben ‘dan takara, su guji kwadayin kudin ‘yan siyasa, su tsaidawa al’umma ‘dan takarar da ya fi cancanta.

A gefe guda kuma irinsu Mukhtar Ramalan Yero da Isa Muhammad Ashiru za su gwabza wajen neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP.

Za a hana Abiodun zarcewa?

Mu na da labari Ayodele Oludiran wanda yana cikin ‘yan jam’iyyar APC a Ogun, ya kai karar gwamnansa, Dapo Abiodun a wajen shugabannin jam'iyyar APC.

Oludiran ya kai korafinsa gaban Sanata Abdullahi Adamu, yana jan kunnensa kan sake ba Abiodun takara domin kuwa ya taba aikata wani laifi a kasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel