2023: Yahaya Bello Ya Shige Gaban Su Tinubu, Ya Fara Biyan N100m Lakadan Kuɗin Fom Ɗin Takara

2023: Yahaya Bello Ya Shige Gaban Su Tinubu, Ya Fara Biyan N100m Lakadan Kuɗin Fom Ɗin Takara

  • Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya zama dan takarar shugaban kasa na farko a jam'iyyar APC da ya fara biyan kudin fom din takara
  • Yemi Kolapo, shugaban kungiyar yakin neman zaben Yahaya Bello ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Kolapo ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, deleget, shugabannin jam'iyyar APC da su yi watsi da abin da zai raba kawuna su aikata abin da zai kawo cigaban jam'iyya da Najeriya

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, zai karbi fom din takarar zabensa a ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Gwamnan ya biya Naira miliyan 100 a safiyar ranar Talata, hakan na nufin shine mutum na farko da a hukumance ya siya fom din takarar shugaban kasa na 2023 a jam'iyyar, a cewar sanarwar da Direktan Watsa Labaran Yahaya Bello Kamfen, Yemi Kolapo ya ce.

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

2023: Yahaya Bello Ya Biya N100m Lakadan, Zai Karɓi Fom Din Takararsa Ranar Laraba
2023: Yahaya Bello Ya Biya N100m, Zai Karɓi Fom Din Takararsa Ranar Laraba. Hoto: DailyTrust.
Asali: Twitter

Gwamnan ya ayyana niyyarsa na neman takarar shugabancin kasar a filin Eagle Square da ke Abuja a ranar 2 ga watan Afrilun 2022.

Yana takarar ne duk da kiraye-kirayen da aka yi na mayar da mulki yankin kudancin Najeriya. Bello ya fito ne daga yankin Arewa ta Tsakiya inda shugaban APC na kasa Abdullahi Adamu ya fito.

Kolapo ya yi kira ga deleget, shugabannin jam'iyya da sauran masu ruwa da tsaki su guji aikata abin da zai kawo rabuwan kawunna

Kolapo cikin sanarwar da ya fitar ya ce:

"Bayan biyan kudin fom din, magoya bayan Gwamna Bello su tabbatar cewa sunansa zai fito a takardan jefa kuri'a na zaben shugaban kasa na 2023. Muna farin ciki da adadin gwamnonin APC, shugabanni da masu ruwa da tsaki da suka nuna goyon bayansu ga mai gidanmu. Muna jadada cewa ba a san shi da cin amana ba. Mutum ne mai cika alkawari kuma Najeriya ce a gabansa.

Kara karanta wannan

Yau Talata APC za ta fara sayar da Fam na takarar zaben 2023

"Duk da cewa a hukumance yanzu ne takarar ta fara, kowa ya sani cewa Gwamna Bello ya dade yana bayyana ra'ayinsa na takara. Ya kuma sake nuna wa cewa da gaske ya ke ta hanyar fara biyan kudin fom."

NAN ta rahoto Kolapo ya kuma yi kira ga deleget da sauran yan Najeriya su yi watsi da duk wani abu da zai raba kan al'umma su saka kishin kasa a gaba.

Har wa yau, ya ce ba su da haufi cewa mambobin Kwamitin Gudanarwa na za su yi abin da zai kawo cigaban jam'iyyar da kasa a yayin aikinsu na zaben wanda zai yi wa jam'iyyar takara.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A baya, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: kwamishinan gwamna Zulum ya yi murabus, zai tsaya takara kujerar yankinsu

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel