Da Naira muke harkalla: APC ta musanta mallakar dalolin da aka sace a ofishinta

Da Naira muke harkalla: APC ta musanta mallakar dalolin da aka sace a ofishinta

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da ikirarin cewa ta rasa damin kudi dala 50,000 a ranar Laraba a hedkwatarta
  • Babban sakataren jam’iyyar na kasa, Barista Felix Morka, ya ce kudin da ya bata ba mallakar jam;iyyar bane
  • Ya kuma ce kudin bai da alaka da kudaden da aka tara daga wajen siyar da fom domin a asusun jam'iyyar ake turawa kuma a naira ake sakawa ba dalar Amurka ba

Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi martani kan sace makudan kudade da aka yi a sakatariyarta na kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda wani jami’in jam’iyyar daga Enugu ya koka cewa an yi masa fashin kudi dala 50,000 a hedkwatar jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

2023: PDP ce dai kadai za ta kai 'yan Najeriya ga tudun mun tsira, inji Saraki

Lamarin ya afku ne kasa da awanni 24 bayan jam’iyyar ta fara sayar da fom din takararta.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, jam’iyyar ta mayar da wajen sayar da fom dinta zuwa babbar cibiyar taro ta kasa da ke Abuja daga sakatariyarta.

Da Naira muke harkalla: APC ta musanta mallakar dalolin da aka sace a ofishinta
Da Naira muke harkalla: APC ta musanta mallakar dalolin da aka sace a ofishinta Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake bayani kan dalilin komawarsu ICC, babban sakataren jam’iyyar na kasa, Barista Felix Morka, ya ce sun yanke shawarar komawa ICC ne saboda saukaka cunkoson jama’a da ababen hawa a kewayen sakatariyar.

Ya kuma yi bayanin cewa $50,000 da aka sace a sakatariyar jam’iyyar na kasa a ranar Laraba ba mallakar jam’iyyar bane, rahoton Vanguard.

Ya ce:

“A ranar Laraba, 27 ga watan Afrilun 2022, an rahoto cewa wani mutum ya yad da kudi kimanin $50,000 a mashigin sakatariyar jam’iyyar.
“Don fayyace gaskiyar lamari, kudin da ya bata ba na jam’iyyar bane. Kudin da ya bata kuma bai da alaka da abun da aka tara daga siyar da fom ko sauya wajen karbar fom din takarar daga sakatariya zuwa ICC, kamar yadda kafofin watsa labarai suka rahoto.

Kara karanta wannan

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

“Kamar yadda aka yayata sannan aka rahoto a manyan jaridu, duk wani fom ana biyan kudinsa ne a asusun bankin jam’iyyar. Kuma ana saka kudin ne a Naira ba wai a dalar Amurka ba.
“Muna umurtan mambobin jam’iyyar da jama’a da su yi watsi da kowani rahoto sabanin haka a matsayin karya da batarwa.”

Barawo ya yi awon gaba da zunzurutun kudi dala 75,000 a hedkwatar APC

A baya mun kawo cewa, an shiga rudani a sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Laraba, 27 ga watan Afrilu, lokacin da zunzurutun kudi har kimanin naira miliyan 43 ya yi batan dabo.

An tattaro cewa an ruguza babban rumfar da a karkashinsa ake siyar da fom din takara ba tare da wani cikakken bayani ba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa jam’iyyar ta yanke shawarar amfani da manyan rumfunar da aka kafa ne saboda aikin gyare-gyare da ake yi a ainahin ginin sakatariyar.

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng