Kai Abokina Ne Amma Ba Zan Maka Aiki Ba, Shugaban PDP Ya Faɗa Wa Atiku
- Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, Dr. Iyorchia Ayu ya sanar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa duk da abokai ne su, ba zai yi masa aiki akan kudirinsa ba
- Ayu ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga Kwamitin Ayyuka na Kasa, NWC, da kuma Kungiyar kamfen din Atiku bayan kai wa ofishin jam’iyyar na kasa ziyara
- Kamar yadda Ayu ya tunatar da shi, sun kai shekaru 30 da sanin juna a matsayin abokai, sai dai abotarsu ba za ta sa ya yi masa aiki shi daya ba, duk ‘yan takara 17 zai yi wa aiki
Abuja - Dr. Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya bayyanawa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa duk da abokai ne su, ba zai yi masa aiki a matsayinsa na dan takara ba, Daily Trust ta ruwaito.
Yayin jawabi ga mambobin Kwamitin Ayyuka na Kasa, NWC da kuma kungiyar kamfen din tsohon mataimakin shugaban kasar bayan kai ziyara ofishin jam’iyyar na kasa.
Ya ce sun zarce shekaru 30 suna abota
Kamar yadda ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ina son tunatar da batun cewa ni da kai abokai ne na tsawon shekaru fiye da 30, mu ne jagororin SDP lokacin Cheif MKO Abiola.
“Yau ka gabatar da kanka a matsayin dan takarar shugaban kasa. Ina son ka san cewa har yanzu abokan juna ne mu, ba zan musanta wannan batun ba.
“Mun yi ayyuka daban-daban a matakai iri-iri, mun yi aiki lokacin shugaban kasa Obasanjo. Mulkin da ya tallafa wa Najeriya har ta bunkasa. Mun yi aiki sosai a siyasance duk a tare lokaci ni ne ministan harkokin cikin gida.”
Ya shawarci Atiku da ya dage wurin kamfen
Sahara Reporters ta rahoto yadda ya ci gaba da bayyana cewa duk da alakarsu ta abota, a matsayinsa na shigaban jam’iyya, ba zai yi masa aiki ba. Zai yi wa ‘yan takara 17 aiki.
A cewar Ayu, Atiku ya tallata kansa ya kuma yi aiki tukuru don ba za su goyi bayan wani dan takara ba duk da suna son Atiku kuma suna girmama juna.
Ya ce in har aka ba wani dan takara cikinsu dama yana da tabbacin cewa za su gyara kasar nan fiye da yadda gwamnatin APC ta yi.
Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP
A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.
An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.
‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.
Asali: Legit.ng