Majalisar Adamawa ta ayyana kujerar wani dan majalisa a matsayin babu kowa saboda ya koma APC
- Majalisar dokokin jihar Adamawa ta saka kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Michika, Joseph Ayuba Kwada, a kasuwa
- Wannan hukuncin ya biyo bayan sauya sheka da dan majalisar ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC
- Kakakin majalisar, Rt. Hon Aminu Iya Abbas, ya ce hukuncin ya yi daidai da sashi na 109 1(G) na kundin tsarin mulkin kasar
Adamawa - Kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Rt. Hon. Aminu Iya-Abbas, ya ayyana kujerar dan majalisa mai wakiltan mazabar Michika, Hon. Joseph Kwada, wanda aka fi sani da Depolis, a matsayin babu kowa.
Majalisar ta saka kujerar Kwada a kasuwa ne saboda ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jaridar Punch ta rahoto.
A karshen makon da ya gabata ne Kwada ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP a Michika bayan ya bayyana rashin adalci a matsayin dalilinsa na aikata haka.
Kwada ya kuma kasance dan majalisa na uku da ke sauya sheka zuwa wata jam’iyyar siyasa a karkashin majalisar dokokin jihar mai ci a yanzu.
A kwanan nan ne yan majalisa masu wakiltan Mayo Belwa da Mubi ta Kudu, Ibrahim Italiya da Umar Musa Bororo suka sauya sheka zuwa APC da PDP.
Kakakin majalisar ya ayyana kujerar dan majalisar a matsayin babu kowa bayan wani kudiri da Hon. Pwamwakeno Mackondo, ya gabatar kan haka yana mai nuna ga sashi na 109 (1g) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
TVC News ta rahoto cewa bayan an gabatar da kurin tare da samun goyon baya, sai kakakin majalisar ya ayyana kujerar dan majalisar a matsayin babu kowa sannan ya bukaci magatakardar ya sanar da hukumomin da abun ya shafa hukuncin majalisar ciki harda INEC.
Bayan ya sa labule da Buhari: Ana rade-radin Tambuwal zai sauya sheka daga PDP zuwa APC
A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi wata ganawar sirri tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu.
Ganawar tasu na zuwa ne kasa da mako guda bayan shirin dattawan arewa na tsayar da dan takarar yarjejeniya a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya wargaje.
Sai dai kuma, wannan ganawa da Tambuwal ya bayyana a matsayin na sirri ya haifar da hasashe kan yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP a karo na biyu, jaridar Leadership ta rahoto.
Asali: Legit.ng