Karin bayani: Jigo a majalisa, sanatan PDP daga Sokoto ya sauya sheka zuwa APC

Karin bayani: Jigo a majalisa, sanatan PDP daga Sokoto ya sauya sheka zuwa APC

  • Sanata Ibrahim Abdullahi Danbatta, sanata daga jihar Sokoto ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC
  • Sanatan ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya mika wa shugaban majalisar dattawa a yau Laraba
  • Ahmad Lawa, shugaban majalisar dattawa ne ya bayyana hakan a zaman majalisar da aka yi a yau 27 ga watan Afrilu

FCT Abuja - A yau ne majalisar dattawa ta sanar da cewa, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbatta ya sauka sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Danbatta ya mika wasika ga shugaban majalisa, inda shugaban ya karanta ficewar sanatan daga PDP zuwa APC a zaman majalisar na yau Laraba 27 ga watan Afrilu.

Majalisa dattawa ta karbi takardar barin sanata PDP zuwa APC
Yanzu-Yanzu: Jigo a majalisa, sanatan PDP daga Sokoto ya sauya sheka zuwa APC | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar ta Legit.ng Hausa ta samo daga majalisar ta ce:

"Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar Sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu, Ibrahim Abdullahi Danbaba, inda ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba, ya saya Fom din takara shugaban kasa N100m

Yayin da APC ke ci gaba da jiran ranar zaben fidda gwani, jam'iyyar na ci gaba da samun bakin fuska cikinta a 'yan kwanakin nan.

Bayan ya sa labule da Buhari: Ana rade-radin Tambuwal zai sauya sheka daga PDP zuwa APC

A bangare guda, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi wata ganawar sirri tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, 26 ga watan Afrilu.

Ganawar tasu na zuwa ne kasa da mako guda bayan shirin dattawan arewa na tsayar da dan takarar yarjejeniya a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya wargaje.

Sai dai kuma, wannan ganawa da Tambuwal ya bayyana a matsayin na sirri ya haifar da hasashe kan yiwuwar sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP a karo na biyu, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan ya sa labule da Buhari: Ana rade-radin Tambuwal zai sauya sheka daga PDP zuwa APC

Gwamnan wanda ya kasance daya daga cikin masu neman tikitin shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa baya cikin yan takarar yarjejeniya da kungiyar dattawan arewa karkashin Farfesa Ango Abdullahi suka tsayar.

Sabuwar dokar APC ta baiwa Amaechi, Ngige awanni 72 su yi murabus ko su hakura da takararsu

A wani labarin, mun ji cewa wata sabuwar doka da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) suka saki a ranar Talata, ta tanadi cewa ya zama dole duk masu mukaman siyasa da ke da niyan shiga zaben fidda gwaninta a dukkan matakai su yi murabus akalla kwanaki 30 kafin zaben.

Bisa ga sabuwar dokar, wasu daga cikin yan majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke neman takarar shugaban kasa kamar su ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi da takwaransa na kwadago, Chris Ngige, suna da sauran kwanaki uku kacal su yi murabus ko su hakura da takararsu.

Kara karanta wannan

Za'a yi Tawafi na musamman wa Bola Tinubu a Masallacin Ka'abah don nasara a zabe

Hakan ya kasance ne duba ga cewa zaben fidda gwanin shugaban kasa na APC, zai gudana a tsakanin ranar 30 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni kamar yadda yake a jadawalin jam’iyyar mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel