'Dan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Ya Buƙaci a Canja Wa 'Nigeria' Suna, Ya Koyar Da Yadda Ake Furta Sabon Sunan
- Matashin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, yana so a sauya sunan Najeriya
- Garba ya bukaci a canja sunan zuwa 'Nigritia', wanda ya ce itace asalin sunan kasar kafin turawan mulkin mallaka su sauya ta zuwa Nigeria
- A cewarsa suna shine asali kuma ya bada misali da wasu kasashen Afirka da suka sauya sunanyensu bayan sun samu 'yanci daga turawan mulkin mallaka
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya bukaci a canja wa Najeriya sunanta.
Garba ya wallafa wani rubutu ne a shafinsa na Twitter don nuna damuwarsa.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mene zai hana mu yi wa kasar nan garambawul, mu sauya ta zuwa tarayya na ainihi kuma mu canja sunan kasar suna "Tarayyar Nigritian" ko kuma Nigritia.
"Tunda, asali, Nigritia ne sunan mu kafin Lady Lugard ta canja wa kasar suna zuwa Nigeria.
"Wannan yana cikin tsarin mu da izinin Allah, gwamnatin mu za ta mika wannan bukatar ga majalisar tarayya.
"Lokaci ya yi da za mu raba kanmu daga duk munanan kallo da ake mana, mu sake tsarin rayuwarmu, mu ceto kasarmu daga hannun turawan mulkin mallaka da rabe-raben da ke tsakanin mu don kafa kasa mai hadin kai da hakuri da juna."
Garba ya kuma yi tambaya:
"Idan Ghana za ta iya canja sunan da turawan mulkin mallaka suka bata na Gold Coast, Kenya daga Bristish East Africa, Benin daga Dahomey, Togo daga Togoland da sauransu ... mai zai hana Nigeria ta cigaba da amsa sunan da turawan mulkin mallaka suka sanya mata?
"Mu canja sunan kasar zuwa ainihin sunanta kafin zuwan turawan mulkin mallaka wato Nigritia. Asali shine komai," in ji Garba.
Garba ya koyar da yadda ake furta 'Nigritia'
Hakazalika, Garba, ya yi bidiyo inda ya furta yadda ake fadan tsohon sunan na Nigeria kafin turawan mulkin mallaka su canja sunan.
Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan
A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.
Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.
Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.
Asali: Legit.ng