Tashin Bama-Bamai: Ya Zama Dole Ƴan Najeriya Su Fara Kare Kansu, In Ji Ƙwararru a Ɓangaren Tsaro

Tashin Bama-Bamai: Ya Zama Dole Ƴan Najeriya Su Fara Kare Kansu, In Ji Ƙwararru a Ɓangaren Tsaro

  • Wasu kwararru a bangaren tsaro sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta karfafawa mutanen kasar su rika kare kansu duba da yawaitar hare-haren bam a kasar
  • Tsohon direkta na DSS, Mike Ejiofor da Birgediya Janar Jonathan Temlong (mai murabus), tsohon sojan Najeriya ne suka bada wannan shawarar
  • Kwararrun sun kara da cewa ba su nufin mutane s dauki makamai sai dai su zama masu sa ido sosai kan abubuwa da ke faruwa a unguwanninsu

Wasu kwararru a bangaren tsaro sun yi kira ga yan Najeriya su tashi tsaye su kare kansu a yayin da batun tsaro ke cigaba da tabarbarewa, Daily Trust ta rahoto.

Yayin da ya ke magana a shirin Sunrise na Channels Television, tsohon direkta mai murabus a hukumar DSS, Mike Ejiofor da Birgediya Janar Jonathan Temlong (mai murabus) sun ce Najeriya na komawa ya tamkar 2013 zuwa 2014 lokacin da yan ta'adda ke kai harin bama-bamai.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Tashin Bama-Bamai: 'Ya Zama Dole Yan Najeriya Su Fara Kare Kansu'
Bama-Bamai: 'Ya Zama Dole Yan Najeriya Su Fara Kare Kansu'. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

An kai hare-haren bam guda uku a jihohin Taraba da Yobe a makon da ta gabata kuma kwararru na ganin shirya harin aka yi.

A cewar Temlong, ya zama dole gwamnatin Najeriya ta karfafa wa yan kasar gwiwa su iya kare kansu, rahoton Naija Dailies.

"A matsayin mu na mutane, ya zama dole mu kare kanmu, ya kamata mu rika daukan matakan dakile abu kafin ya faru.

"Ba zai yiwu jami'an tsaro su kasance a ko ina a ko yaushe ba hakan yasa dole yan Najeriya su rika saka idanu sosai.
"Ya zama dole gwamnati ta karfafa wa mutanen kasa gwiwa su iya magance abubuwa irin wannan," in ji shi.

A bangarensa, Ejiofor ya ce yan ta'addan suna tserewa zuwa wasu yankunan saboda ragargazansu da sojoji ke yi daga Borno, suna koma wa arewa maso yamma da tsakiya.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

Ya koka kan cewa yan Najeriya sun saki jikinsu bayan hare-haren bama-bamai na shekarun 2013 da 2014.

Ejiofor ya ce:

"A 2014, mutane sun dauki tsaro a hannunsu ta hanyar saka idanu kan abubuwan da ke faruwa.
"Ya kamatu hukumomin tsaro su zaburar da mutane game da sa ido akan abubuwan da ke faruwa. Ba mu ce mutane su dauki makamai ba, muna cewa ne su rika lura da abin da ke faruwa a unguwanninsu."

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel