An damke matashin da ya damfari Sarki a Kwara sama da N33.4m

An damke matashin da ya damfari Sarki a Kwara sama da N33.4m

  • Jami'an hukumar EFCC sun cika hannu da wani matashi da ya damfari Sarki mai daraja ta 1 a jihar Kwara
  • Sarkin ya shigar da karan matashin da abokansa bayan sun amshi sama da milyan talatin da uku a hannunsa
  • Kakakin hukumar yace za'a gurfanar da shi bayan kammala bincike kuma ana cigaba da kokarin damke sauran

Abuja - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta bayyana cewa jami'anta sun damke wani mutumi wanda ya damfari Sarkin Okuta, a jihar Kwara N33,399,999.

Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, a jawabin da ya saki a ranar Litinin, ya ce mutumin mai suna Fidelis Poor, ya damfari Sarkin gargajiya ta hanyar ce masa yana da kwantena dake bakin teku.

Kara karanta wannan

Duk a cikin aiki ne: Jami'an kwana-kwana sun ceto zakaran da ya fada rijiya

Sarkin, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne yace sun bukaceshi ya biya kudi don a fitar da kwantenan a Abuja.

Jawabin yace:

"Hukumar EFCC ta damke wani Fidelis Poor, ya hada baki da wasu wajen damfarar wani Sarkin Gargajiya mai matai na daya a jihar Kwara, Mai Martaba Idrs Sero Abubakar, kudi N33,399,999,”
"(Fidelis) Poor ya hada kai da wasu wajen damfarar Sarkin ta hanyar ce masa yana da kwantenan kaya a tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja don amfanin al'ummar masarautarsa."

An damke matashin da ya damfari Sarki a Kwara sama da N33.4m
An damke matashin da ya damfari Sarki a Kwara sama da N33.4m Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Uwajuren ya kara da cewa bayan biyansu kudi miliyoyi, bai ga kaya ba kuma basu dawo masa da kudinsa ba.

Sai hukumar ta kaddamar da bincike kan lamarin kuma suka samu nasarar damke FIdelis, sauran kuma ana nemansu har yanzu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Yace za'a gurfanar da shi bayan kammala bincike kuma ana cigaba da kokarin damke sauran, Kakakin ya kara.

EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta titsiye wani dan tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura bisa zargin sayan kadara ta Naira miliyan 130.

Majiyoyi daga hukumar da suka samu bayanai kan lamarin amma aka hana su shaida wa manema labarai, sun ce Amir Al-Makura mai shekaru 24, ya biya tsabar kudi Naira miliyan 96 “da kudin kasashen waje” a matsayin kudin wani bangare na kadarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel