Rigima za ta kaure saboda ‘taba’ sunayen masu tsaida 'Dan takarar Shugaban kasa a APC

Rigima za ta kaure saboda ‘taba’ sunayen masu tsaida 'Dan takarar Shugaban kasa a APC

  • Akwai kishin-kishin din samun rashin jituwa tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Hakan yana zuwa ne a sa’ilin duka wasu jam’iyyan siyasa su ke shirin gudanar zaben fitar da gwani
  • Idan shugabannin jam’iyya ba su sa baki ba, za a iya samun matsala wajen zaben tsaida ‘dan takara

Abuja - Tribune ta ce za a iya samun kalubale a kan batun zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa da APC za ta gudanar a karshen watan Mayun 2022.

Akwai ‘yan jam’iyyar ta APC mai mulki da suke zargin cewa za a taba jeringiyar sunayen da shugabanni na reshen jihohi za su gabatar a sakatariya.

Ana tunanin za a iya cusa sunayen wadanda bai dace su shiga zaben fitar da gwani ba a jerin da za a kai Abuja, ganin irin adadin masu yin zaben gidan.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Rahoton ya ce kimanin mutum 7800 ake lissafin za su kada kuri’a wajen fito da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben da za ayi nan da makonni biyar.

Tsakanin 7 zuwa 9 ga watan Mayun 2022 jam’iyyar APC za ta zabi wadanda za su kada kuri’a domin a tsaida ‘yan takara a matakin jihohi da na kasa.

Korafin da ake yi shi ne takardar da za a kai wa uwar jam’iyya na dauke da sunayen wasu da sun sauya-sheka daga APC ko ba su da lafiya, ko ma sun mutu.

Shugaban kasa a APC
Shugaban kasa Buhari a taron APC NEC Hoto: OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Sashe na 12.1 (v) na tsarin mulkin APC ya sa tsofaffi da ‘yan majalisar tarayya masu ci da shugabannin majalisar dokoki a cikin masu fito da ‘yan takara.

Wasu jihohin da ake zargin za ayi rikici

Kara karanta wannan

Jigon APC ga 'yan takara: Kunsan ba ku da N100m me ya kai ku takara a jam'iyyar APC

Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa zai yi wahala a gudanar da wannan zabe a wasu jihohi saboda irin kwamacalar da suka cika APC a jihohi.

Rigima ta kaure tsakanin ‘ya ‘yan APC na reshen jihar Oyo, har sai da ta kai uwar jam’iyya ta tsoma baki. Yanzu haka wannan rikici ya shiga wasu jihohi.

Sauran jihohin da aka samu wannan matsala a game da sunayen masu fito da ‘dan takara akwai Benuwai, Filato, Ogun, Ribas, Imo, Zamfara, Legas da Kano.

An samu matalsa tun lokacin Mala Buni

Wasu na kukan sunayen da aka kai wa kwamitin rikon kwarya na Mai Mala Buni kwanakin baya, cike yake da wasu mutanen da ba su cancanta da zabe ba.

Ana zargin an hada kai da jami’an gwamnati ne an kara sunayen wasu a jerin. Masu neman mulki kan yi haka domin su yi nasarar samun takara a jam’iyya.

Gwamna Wike na neman tutan PDP a 2023

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

A jiya ne aka ji Gwamna Nyesom Wike ya yi rabon N200m a Kaduna, ya bar tsofaffin ma’aikatan jihar Ribas su na kukan cewa rabonsu da fansho tun a 2014.

Mai neman takarar shugaban kasar ya roki ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP na reshen jihar Kaduna su ba shi 80% na kuri’unsu a zaben fitar da gwani da za a gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng