Wike ya rabawa 'Yan IDP N200m a Kaduna, ya bar tsofaffin ma'aikata babu fansho a jiharsa

Wike ya rabawa 'Yan IDP N200m a Kaduna, ya bar tsofaffin ma'aikata babu fansho a jiharsa

  • Gwamnan jihar Ribas ya yi zama da shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Kaduna a ranar Litinin
  • Nyesom Wike ya roki ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayyar su mara masa baya a zaben shugaban kasa
  • Wike ya bada kyautar kudi a Kaduna, a lokacin da tsofaffin ma’aikatan Ribas ke neman hakkinsu

Kaduna - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bada sanarwar kyautar Naira miliyan 200 ga wadanda matsalar rashin tsaro ta rutsa da su a jihar Kaduna.

The Cable ta ce Mai girma Nyesom Wike ya sanar da haka a lokacin da ya ziyarci garin Kaduna domin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Nyesom Wike ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyya da za su kada kuri’a wajen fito da ‘dan takarar PDP a zaben shugaban Najeriya su ba shi kashi 80% na kuri’unsu.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Gwamnan jihar Ribas ya yi jawabi a sakatariyar PDP da ke garin Kaduna, inda ya ce yana neman ‘ya ‘yan jam’iyya 60 su zabe shi a matsayin ‘dan takaransu.

Wike ya ce idan mutane 60 sun zabe shi, ragowar 18 da suka rage sai su zabi sauran ‘yan takara. Mutum fiye da 10 su ke neman tikitin shugaban kasa a PDP.

Jaridar Daily Trust ta rahoto mai neman mulkin yana cewa jam’iyyar hamayya ta PDP na bukatar wanda zai iya karbe mulki daga hannun APC, ya ceto Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan Ribas
Nyesom Wike wajen kamfe Hoto: @riversgovernmenthouse
Asali: Facebook

Shugabanni sun gaza - Wike

“Ba sabon labari ba ne halin da kasarmu ta samu kan ta a mulkin APC. Misali ku duba yanayin da ake yau. A da, Kaduna na cikin inda aka fi samun tsaro."
“Mutane su kan yi tafiya zuwa Kaduna hankali kwance, babu shugaba a Arewa da zai ce bai da gida a Kaduna, mutane kan baro Abuja cikin dare, su zo Kaduna.”

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

“A lokacin da na ke Minista, a mota na zo garin nan, amma abin da ke faruwa a yau sun nuna cewa Kaduna ta rasa kimarta, saboda sakacin wadanda ke mulki.”

Saboda haka gwamnan ya bada gudumuwar N200m ga wadanda wannan matsala ta shafa a Kaduna.

Tsohon gwamna Sanata Ahmed Makarfi ya yabi Wike, yace da zai iya da ya ba shi mulki, saboda yadda ya taimakawa PDP a lokacin da ta ke cikin matsala.

'Yan fansho na wayyo Allah

Kyautar Nyesom Wike ta zo ne ‘yan kwanaki bayan an ji labari tsofaffin ma’aikata sun yi zanga-zanga a gidan gwamnatin Ribas saboda rashin biyan su fansho.

Dattawan sun ce tun da gwamnatin Wike ta karbi mulki a Mayun 2015 ba a biya su kudin fansho da na sallama da sauran hakkokinsu na barin aikin gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel