Malamin Addini: Mutane 2 ne kadai masu kyakkyawar manufa cikin masu son gaje Buhari
- Gabanin zaben shekarar 2023, Fasto Henry Ojo ya bayyana masu neman shugabancin Najeriya da ya kamata a kadawa kuri'u
- Shugaban na Cocin Christ Apostolic ya ce Allah ya nuna masa mutum biyu ne kadai a cikin ’yan takarar shugaban kasa na gari
- Fasto Ojo ya ce mutum biyun dai su ne; mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamna Nyesom Wike kuma ya shawarci ‘yan Najeriya da su zabi daya daga cikinsu
Ibadan, jihar Oyo – Fasto Henry Ojo, shugaban Cocin Christ Apostolic na Arogungbogunmi, ya ce Allah ya nuna masa cewa ‘yan takarar shugaban kasa biyu ne kadai a cikin wadanda suka bayyana aniyarsu na gaje Buhari ke da kaunar Najeriya a zuci.
Malamin ya ce daya daga cikin wadanda yake magana akai ya fito daga Kudu maso Yamma yayin da dayan kuma dan Kudu maso Kudu ne, inji rahoton The Punch.
Legit.ng ta tattaro cewa Fasto Ojo ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu, a wajen wani taron tattaunawa kan abin da ya kira ‘Shedding light on the mind of God to Nigerians’ a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
A kalamansa:
“Daga cikin dukkan masu neman shugabancin kasar nan da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takara a zaben 2023, Allah ya nuna min guda biyu ne kawai ke iya jan ragamar kasar.
“Mutum na farko dan Kudu maso Yamma ne yayin da mutum na biyu ya fito daga Kudu maso Kudu, daya daga cikin mutanen biyu shi ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayin da na biyun kuma shi ne Nyesom Wike.”
Shugaban kasa a 2023: Osinbajo, Wike za su taka rawar gani idan aka zabe dayansu
Fasto Ojo ya ce Allah ya nuna masa ‘yan Najeriya za su sha romon dimokradiyya a karkashin mulkin mataimakin shugaban kasa Osinbajo idan suka bashi dama, kamar yadda Independent ta tattaro.
A cewarsa:
“Allah ya nuna min cewa Osinbajo zai yi abin kirki idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa. A karkashin gwamnatinsa, Allah ya nuna min ‘yan kasa za su sha romon dimokuradiyya kuma kasa za ta kubuta daga kangin wahala.
“A daya bangaren kuma, Allah ya ce min ya sanya himma wajen yi wa Najeriya hidima a zuciyar Nyesom Wike. Wannan yana nuna cewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai yi aiki nagari. A karkashinsa, kasar za ta ga ci gaba."
Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki
A wani labarin, Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Legit.ng ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.
Gwamnan na jihar Adamawa ya ce Atiku na da dukkan abubuwan da ya kamata na mulkin Najeriya, yana mai jaddada cewa zai yi kokarin ganin ya zama shugaban Najeriya idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng