2023: Tinubu ya caccaki Buhari, Shugabannin Najeriya yayin yi wa matasa kamfe
- Asiwaju Bola Tinubu ya kaddamar da yakin neman zabensa ga matasan jam’iyyar APC a jihar Legas
- ‘Dan siyasar ya soki shugabannin da aka yi, ya yi ikirarin duk sun gasa cika alkawuran da suka yi
- An ji Tinubu ya kara nanata maganar cewa katin PVC su na tashi aiki idan har ba a sabunta su ba
Lagos - Asiwaju Bola Tinubu ya soki shugabannin da ke mulki a kasar nan, ya yi alkawarin cewa zai magance matsalolin Najeriya idan ya karbi mulki.
Jaridar Premium Times ta rahoto Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu 2022, ya na cewa shugababbi sun gaza cika alkawuransu.
Da yake yi wa wasu matasa jawabi a Legas, an ji ‘dan siyasar yana jifan shugabannin da aka yi a Najeriya da kin cika alkawuran da suka yi wa talakawa.
A jawabin na sa, Bola Tinubu bai bambamce tsakanin gwamnatin APC da Muhammadu Buhari yake jagoranta da kuma gwamnatocin PDP da aka gada ba.
Rashin cika alkawura
“Mu na fahimtar fushinku a lokacin da ranku ya baci, ba na zargin ku da laifi. Alkawuran da aka rika yi maku a baya ne ba a cika ba.”
“An yi maku alkawarin gobe za ta yi kyau. Ba za mu cigaba da kuka kan abin da ya wuce ba.”
- Bola Tinubu
Matasan Najeriya malala ne?
Baya ga batun cika alkawari, jaridar ta ce tsohon gwamnan na Legas ya dura kan shugaba Muhammadu Buhari kan kiran matasa malalata da ya taba yi.
“Ba za mu cigaba da yi wa gazawar NEPA (kamfanonin lantarki) uzuri ba. Babu kasar da za ta iya cigaba ba tare da an samu wutar lantarki ba."
A ba mu wuta, idan ba mu dace ba, sai a zage mu. Amma ba zai yiwu a hana mu wuta ba, sannan a zarge mu da cewa mu malalata ne.”
- Bola Tinubu
A cewar Tinubu, akwai isasshen gas da zai sa a samu lantarki, har a iya saidawa kasashen Turai domin a samu kudi. Bayaninsa na nuna an gagara gyara wuta.
Sai an sabunta katin zabe a 2023?
PVC zai tashi aiki
Har ila yau, an ji Tinubu ya kara nanata batun tashi-aikin katin zabe na PVC, inda ya yi kira da matasan da su tabbatar da cewa katinsu bai tsufa daga aiki ba.
“Idan ba ku da PVC, ko ba a tantance katin ba, ba ka da tabbacin cewa (katin) bai tashi aiki ba. Ka da ku manta yana da iya lokacin da yake daina yin aiki.”
- Bola Tinubu
Gwamnati ta yafewa marasa gaskiya
A 2013 gwamnatin Goodluck Jonathan ta yafewa tsohon gwamnan Bayelsa, Diepriye Alamieyeseigha laifin satar dukiyar talakawa daga baitul mali.
A wancan lokaci, an ji cewa irinsu Nasir El-Rufai ya yi kaca-kaca da shugaba Goodluck Jonathan. Sai ga shi gwamnatin Buhari ta yi irin wannan afuwar a yau.
Asali: Legit.ng