Yafewa Nyame da Dariye ta jawo Jami’an EFCC, ICPC su na jifan Shugaban kasa da zargi

Yafewa Nyame da Dariye ta jawo Jami’an EFCC, ICPC su na jifan Shugaban kasa da zargi

  • Ma’aikatan da suka saida ransu a EFCC da ICPC sun yi tir da yafewa Jolly Nyame da Joshua Dariye
  • Bayan tsawon shekara da shekaru ana shari'a, Shugaban kasa ya yi wa wadanda aka samu da laifi afuwa
  • Lauyoyi, jami’ai da kungiyoyi masu zaman kan su su na ganin an kawowa yaki da rashin gaskiya cikas

Jami’an hukumomin EFCC da ICPC sun bayyana cewa gwiwowinsu sun sare bayan jin cewa shugaban kasa ya yi wa Jolly Nyame da Joshua Dariye afuwa.

A makon da ya wuce Muhammadu Buhari ya yafewa tsofaffin gwamnonin da aka samu sun yi sata. Premium Times ta nemi jin ta bakin jami’an EFCC da ICPC.

Rahoton da aka fitar ya bayyana cewa a hirar da aka yi da su, ma’aikatan sun ki bari a kama sunayensu, amma sun nuna takaici kan matakin da aka dauka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa

Wani jami’in EFCC yake cewa:

“Mu kan ce matsalar da muke samu wajen yaki da rashin gaskiya ta na bangaren shari’a ne, amma yanzu mun ga matsala daga wajen shugaban kasa.”

Ma'aikata sun yi zugum

Akwai wani ma’aikacin hukumar EFCC ko ICPC da ya ke cewa yanzu su na zuwa ofis, su karbi albashi ne kurum ba tare da su na sha’awar aikin da suke yi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa yafewa wadannan tsofaffin gwamnoni da kotu ta daure, ya bata sunan Buhari da yake ikirarin ya na yaki da rashin gaskiya.

Shugaban kasa
Shugaban kasa da Shugaban EFCC, Bawa Hoto: Twitter
Asali: Facebook

“Mutane za su rika yi mana ba’ar cewa shugaban kasa zai iya yafewa babban barawon da mu ke shirin mu gurfanar a gaban kotu.” – inji wani jami’in.

An yi shekara 10 ana wahalar banza

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

Ran ma’aikatan hukumomin biyu da ke yaki da rashin gaskiya da barayin gwamnati ya baci sosai saboda yadda wahalar shekarun da suka sha ta tafi a banza.

Wasu na ganin ba su da katabus da za su cigaba da kokarin yakar barayi a irin wannan yanayi da suke sadakar da ransu, su yi watsi da duk wani tayin cin hanci.

Wannan mataki bai yi kyau ba

A halin yanzu wasu na ganin Mai girma Muhammadu Buhari bai auna matakin yi wa wadannan tsofaffin gwamnoni afuwa ba, domin ya bar masa bakin tabo.

Shugaban kungiyar nan ta CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani ya bukaci a sake duba wannan afuwa musamman a lokacin da aka fara hangen hadarin zaben 2023.

Haka babban lauya mai kare hakkin Bil Adama, Mike Ozekhome SAN ya yi soki wannan lamarin.

A makon jiya aka tabbatar da majalisar kolin kasa ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye, da su ke daure.

Kara karanta wannan

Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari

Gwamna Nyesom Wike ya soki wannan lamari, hakan ta sa aka ji kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya na cewa sukar da gwamnan ya yi bata da wata fa’ida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel