Buhari ya jawo an taso El-Rufai a gaba saboda kalaman da ya yi shekaru 9 da suka wuce

Buhari ya jawo an taso El-Rufai a gaba saboda kalaman da ya yi shekaru 9 da suka wuce

  • Gwamnatin Jonathan ce ta yafewa tsohon gwamnan Bayelsa Diepriye Alamieyeseigha laifin da ya yi
  • A wancan lokaci, Nasir El-Rufai ya yi kaca-kaca da shugaba Goodluck Jonathan kan wannan mataki
  • Ganin gwamnatin APC ta yi irin wannan afuwa yau, an tunawa Gwamnan jihar Kaduna kalamansa

Nigeria - Jama’a su na ta caccakar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a dalilin wasu maganganu da aka taba ji ya fito ya yi a shekarun baya.

Nasir El-Rufai ya na cikin wadanda suka soki Goodluck Jonathan a lokacin da gwamnatinsa ta yi afuwa ga tsohon gwamna, Cif Diepriye Alamieyeseigha.

A wani bidiyo da yanzu aka kakkabe, an ji Malam Nasir El-Rufai ya na sukar shugaban kasa na wannan lokaci saboda afuwar da ya yi wa mai gidansa.

Alamieyeseigha wanda Goodluck Jonathan ya zama masa mataimakin gwamna a Bayelsa ya samu ‘yanci bayan an daure shi a gidan kurkuku a 2013.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

Da Goodluck Jonathan ya zama shugaban Najeriya, sai ya yafe masa laifin na sa, aka fito da shi. An soki gwamnatin tarayya sosai kan wannan a lokacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalaman El-Rufai a 2013

Gwamnan jihar Kaduna na yanzu wanda a lokacin yana ‘dan adawa, ya yi Allah-wadai da hakan. A halin yanzu da APC ke mulki, sai ga shi an yi irin haka.

Nasir El-Rufai da Shugaba Buhar
Gwamna El-Rufai tare da Shugaban kasa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC
“Babu wanda ya ce ayi maganin rashin gaskiya gaba daya, amma ba za a je ana yafewa mutanen da aka daure ba.”
“Mutanen da kotun mu suka same su da aikata laifin rashin gaskiya, sai kuma ace ana yaki da barayin gwamnati.”
“Ana gurbata tunanin marasa gaskiya da kuma yaran masu tasowa da za su ga cewa satar dukiyar kasa akwai riba.”

- Nasir El-Rufai

Buhari ya yi koyi da Jonathan?

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Malam El-Rufai ya yi ikirarin kafin Jonathan, babu wani shugaban kasar da ya taba yafewa wadanda suka yi sata, sai ga shi abin ya maimaita kan shi.

Wani malamin jami’a ya shaidawa Legit Hausa cewa dama abin da ya ragewa gwamnatin APC shi ne yaki da rashin gaskiya, kuma an fahimci duk bula ce.

“Babu wani abin kirki da ya ragewa shugaban kasar nan. Sha’anin tsaro ya tabarbare, haka ilmi, ya watsa mana kasa a ido bayan ya yi mana alkawari."
“Ya yi afuwa ga mutanen da kotu uku ta same su da laifi. A tunani na, sai a soke EFCC da ICPC domin ba su da wani amfani kuma a kasar nan.”

Dariye Da Nyame sun sha

A makon jiya majalisar koli ta kasa ta amince a yafewa wasu mutane, har da tsofaffin gwamnonin Taraba da Filato; Jolly Nyame da Joshua Dariye.

Wasu sun tunawa El-Rufai maganganun da ya yi da aka saki Diepriye Alamieyeseigha, ganin cewa a wannan karo tsofaffin gwamnoni biyu aka yi wa afuwa.

Kara karanta wannan

Yafewa Dariye da Nyame: Fadar shugaba Buhari ta mayarwa Wike da zazzafan martani, ta ce yana ihu ne bayan hari

Asali: Legit.ng

Online view pixel