Da Dumi-Dumi: Daga Karshe, Minista Ngige ya ayyana shiga takarar shugaban kasa, ya faɗi wasu kalmomi
- Bayan dogon lokaci ana yaɗa jita-jita, Ministan Kwadugo da samar da aikin yi, Chris Ngige, ya ayyana shiga tseren gaje Buhari
- Dakta Ngige, wanda ya yaba wa gwamnatin APC, ya ce shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai ba mutane kunya ba
- Ya ce duba da albarkatun ƙasa da Buhari ya taras, ya yi wa yan Najeriya ayyukan raya ƙasa da yawan gaske
Anambra - Daga ƙarshe dai Ministan Kwadugo da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya ayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar shugaban ƙasa a hukumace.
Daily Trust ta rahoto cewa Ministan wanda zai nemi takarar karkashin APC, ya ce jam'iyya mai mulki ba ta gaza ba kamar yadda wasu ke tunani.
Ngige, yayin da yake jawabi gaban dandazon magoya bayan a mahaifarsa Alor dake ƙaramar hukumar Idemili ta arewa a jihar Anambra, ya ce shugaban ƙasa Buhari bai ba mutane kunya ba.
A cewar Ministan, shugaban ƙasa Buhari ya yi namijin ƙoƙari duba da arziƙin ƙasa da ya samu, dan haka be gaza ba.
Vanguard ta rahoto Ngige ya ce:
"Wasu mutane suna cewa wannan gwamnatin ta gaza, sun manta gwamnatin ce ta gina babbar hanyar Enugu-Onitsha, da hanyar Enugu-Porthacourt, ta dawo da martabar masana'antar jiragen sama."
"Gwamnatin ce ta gina layukan dogo da sauran wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a faɗin Najeriya waɗan da sun wuce ka kira su gazawa. Buhari ya yi aiki gwargwadon abin da ya taras a Asusu."
Menene babbar manufarsa ga yan Najeriya?
Dakta Ngige ya ce idan yan Najeriya suka ba shi dama ya ɗare madafun iko, zai zama shugaban ƙasan da kowane ɗan Najeriya zai yi alfahari da shi.
Bugu da ƙari ya ce ya tattara duk wata kwarewa da cancantar zama magajin shugaba Buhari, inda ya ƙara da cewa yanayin da ake ciki yanzun ƙara masa daukaka ya yi.
"Idan na zama shugaban ƙasa na san yadda zan shawo kan yanayin da ake ciki" inji Ministan.
A cewarsa, a matsayinsa na minista ya warware matsalolin ma'aikata guda 1,383, kuma hakan ya ɗaga darajar kwadugo a Najeriya zuwa matakin ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa:
"Ni ba zakaran cikin gida bane ƙadai, ni mutum ne na ƙasa da ƙasa. Game da bukatar ku ta na tsaya takarar shugaban ƙasa, na yi alƙawarin zan yi shawara, sannan na ba da amsa a watan Afrilu."
"A yau, ina mai ayyana cewa Ni, Dakta Chris Nwabueze Ngige, zan tsaya takarar shugabancin Najeriya."
A wani labarin kuma Kwamishinoni uku da hadiman gwamna mai ci sun sauya sheka zuwa PDP a jiha ɗaya
Guguwar sauya sheƙa ta shiga cikin majalisar kwamishinoni da sauran hadiman gwamnatin jam'iyyar PDP a jihar Oyo..
Kwamishinoni uku da wasu hadiman gwamna Seyi Makinde sun sauya sheka daga ADC zuwa PDP mai mulkin jiha.
Asali: Legit.ng