Kwamishinoni uku da hadiman gwamna mai ci sun sauya sheka zuwa PDP a jiha ɗaya

Kwamishinoni uku da hadiman gwamna mai ci sun sauya sheka zuwa PDP a jiha ɗaya

  • Guguwar sauya sheƙa ta shiga cikin majalisar kwamishinoni da sauran hadiman gwamnatin jam'iyyar PDP a jihar Oyo
  • Kwamishinoni uku da wasu hadiman gwamna Seyi Makinde sun sauya sheka daga ADC zuwa PDP mai mulkin jiha
  • A cewar masu sauya shekan sun ɗauki matakin ne bayan zaman tattaunawa da shugabannin ADC reshen Oyo

Oyo - Kwamishinoni uku da wasu masu rike da muƙamai na siyasa da dama na jam'iyyar ADC da suke aiki a gwamnatin gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo sun sauya sheƙa zuwa PDP.

Kwamishinan yaɗa labarai, al'adu da wuraren buɗe ido, Wasiu Olatunbosun, wanda ya jagoranci tawagar masu sauya shekan ne ya sanar da haka a wurin taron manema labarai a Ibadan ranar Talata.

Premium Times ta rahoto cewa kwamishinan ya samu rakiyar kwamishinan noma, Adebiyi Adebisi, da mashawarci na musammna kan kasafi da tsare-tsare, Gbenga Oyekola, zuwa wurin taron.

Kara karanta wannan

Mutanen dake ɗaukar nauyin yan bindiga a jihata, Gwamnan APC ya fasa kwai

Jam'iyyar PDP ta samu karɓuwa.
Kwamishinoni uku da hadiman gwamna mai ci sun sauya sheka zuwa PDP a jiha ɗaya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwamishinan Makamashi, Seun Ashamu, shi ne na uku a majalisar gwamnatin Makinde daga ADC, wanda kuma bai samu halartan wurin taron manema labaran ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa suka sauya sheƙa zuwa PDP?

Mista Olatunbosun ya ce sun ɗauki matakin komawa PDP ne bayan zaman tattaunawa da neman shawari da shugabannin tsohuwar jam'iyyar su ADC na Oyo.

Ya bayyana cewa mai girma gwamna ya cika duk alƙawurran da ya ɗaukarwa ADC kuma ya jawo mambobinta ya naɗa su muƙamai a gwamnatinsa.

Kwamishinan ya kuma kara da share tantamar cewa sauya shekar da suka yi ba zai shafin tsarin zubin jam'iyyar ADC ba ko kaɗan, leadership ta ruwaito.

Ya ce:

"Zamu sanar da matsayar jam'iyyar ADC ga al'ummar jihar mu nan ba da jimawa ba a lokacin da za'a karɓi sauya shekar mu a hukumance."

Kara karanta wannan

Sunaye da jihohi: Kwamishinoni 53 sun yi murabus, ministocin Buhari masu takara sun yi mirsisi

NAN ta tattaro cewa baki ɗaya mambobin ADC da gwamna Makinde ya naɗa a faɗin kananan hukumomi 33 na jihar sun halarci wurin taron.

A wani labarin kuma Sanata Mai Wakiltar Mazabar Shugaba Buhari ya fice daga APC, ya koma PDP

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Katsina ta arewa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Babba Kaita ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.

Bayanai sun nuna cewa Sanata Babba Kaita ya miƙa takardar murabus daga APC a gundumarsa dake ƙaramar hukumar Kankiya ta jihar Katsina ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, 2022.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel