APC ta ƙara wani babban rashi na jigonta, Tsohon Ministan Buhari ya yi murabus daga jam'iyyar

APC ta ƙara wani babban rashi na jigonta, Tsohon Ministan Buhari ya yi murabus daga jam'iyyar

  • A yan kwanakin nan jam'iyyar APC na cigaba da samun koma baya duba da yadda wasu jiga-jiganta ke sauya sheka a wasu sassan ƙasar nan
  • A yau Talata, tsohon Ministan Buhari, Solomon Dalung, ya mika takardar ficewa daga jam'iyya ga mahukuntan APC
  • Ministan ya kafa hujjarsa da yawan rikicin da ake samu a cikin jam'iyya mai mulki, a cewarsa babu amfanin ya cigaba da zama

Plateau - Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress wato APC mai mulki, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Dalung, wanda ya yi aiki karkashin mulkin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a zangon farko, ya tabbatar da haka ne a wata takardar murabus daga APC da ya miƙa wa shugaban jam'iyya.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Bayanai sun nuna cewa tsohon ministan ya miƙa takardar ne ga shugaban APC na gundumar Sabon Gida, karamar hukumar Langtang a jihar Filato.

Tsohon ministan wasanni, Salomon Dalung.
APC ta ƙara wani babban rashi na jigonta, Tsohon Ministan Buhari ya yi murabus daga jam'iyyar Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Takardan mai kwanan watan 1 ga watan Afrilu, fitaccen ɗan siyasan ya rattaɓa hannu a cikinta ranar 18 ga watan Afrilu, 2022, har ta kai ga hannun manema labarai ranar Talata.

Premium Times ta rahoto wani sashin takardan ya ce:

"Ina mai isad da sakon murabus ɗina daga jam'iyyar APC daga ranar nan da na sanar da haka."
"Na yi haka ne duba da abubuwan dake faruwa na rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyya waɗan da suƙa saɓa tsarin siyasa ta na girmamawa da kuma biyayya.
"Sabida haka, demokaraɗiyyar cikin gida ta na da matuƙar muhimmanci wajen tsira da sauke nauyin da mulkin demokariɗiyya ya ɗora wa jam'iyya, idan ba bu haka ba da gudummuwa ya zama mara amfani."

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa 'yan APC ke kara yawan mabiya a Najeriya, inji ministan Buhari

Dalung na ɗaya daga cikin ministocin shugaba Buhari a wa'adinsa na farko tsakanin 2015 zuwa 2019, waɗan da ba su sake komawa kujerunsu ba.

Jarumin Kannywood ya fito takara a PDP

A wani labarin kuma Jarumin Kannywood Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, yan Najeriya dake da niyyar tsayawa takara na cigaba da faɗa wa duniya aniyarsu.

A masana'antar Kannywood , Jarumi Lukman na Labari na ya bayyana tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya daga Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel