Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na ci gaba da tuntuban yan arewa a kokarinsa na son ganin ya gaje Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023
- Wike ya ziyarci takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Ganduje a ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu
- Sai dai Ganduje ya kalli Wike cikin ido sannan ya sanar masa cewa ba zai kai labari ba a zaben
- Amma kuma ya ce yana birge shi saboda irin karfin gwiwar da yake da shi domin hakan ne zai basa damar sake gwada sa'arsa a gaba
Kano – Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalli takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike a cikin ido sannan ya sanar masa da cewa ba zai yi nasara ba a kokarinsa na son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.
Ganduje ya yi sakin zancen ne a lokacin da Wike ya ziyarci jiharsa a yayin da yake ci gaba da tuntubar al’umman yankin arewacin Najeriya domin samun goyon bayansu.
Sai dai kuma cike da barkwanci, Gwamna Ganduje ya ce Wike na birge shi saboda kasancewarsa daga cikin mutane masu karfin gwiwa, wanda koda sun fadi a yau za su sake tashi domin sake gwada sa’arsu a gaba.
A cikin wani bidiyo wanda tuni ya karade yanar gizo, an jiyo Ganduje yana cewa:
“Wato, ka zo ganin yan uwanka maza da mata. Ya yi kyau. Kana neman takarar shugaban kasar Najeriya. Mun ga kokarinka.
“Sannan a karshe, za ka sha kaye, amma za ka zama mai karban faduwa da zuciya dana. Ina son masu karban faduwa da zuciya daya saboda suna da karfin gwiwa. Kuma tunda kana yin abun cikin lumana, za ka yi nisan kwana domin sake gwadawa. Ina taya ka murna, Mai hikima Wike. Nagode kuma Allah ya yi maka albarka.”
Kalli bidiyon a kasa:
2023: Wike zai jikawa kowa aiki a PDP, ba zai janyewa wani takarar da yake yi ba
A wani labarin, mun ji cewa Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan a fito da ‘dan takarar shugaban kasa ta hanyar maslaha ba.
Daily Trust ta rahoto Mai girma Nyesome Wike ya na wannan bayani a garin Kalaba, jihar Kuros Riba.
Nyesome Wike ya kai ziyara zuwa Kalaba ne a yunkurin da yake yi na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP game da batun takarar da zai yi.
Asali: Legit.ng