Tikitin takarar shugabancin kasa: Tinubu da Amaechi na rubibin wakilan doka 3,000 na APC

Tikitin takarar shugabancin kasa: Tinubu da Amaechi na rubibin wakilan doka 3,000 na APC

Kafin zuwan zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da za a yi a ranar 29 ko 30 na Mayun shekarar nan, manyan 'yan takarar kujerar shugabancin kasa sun fara shirya yadda za su yi nasara tare da yin caraf da tikitin takara na jam'iyyar.

Binciken Sunday Tribune ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigon jam'iyyar APC, Sanata Bola Tinubu da ministan sufurin jiragen sama, Rotimi Amaechi, suna kokari fiye da sauran 'yan takara wurin samun kuri'un wakilan doka na jam'iyyar.

Tikitin takarar shugabancin kasa: Tinubu da Amaechi na rubibin wakilan doka 3,000 na APC
Tikitin takarar shugabancin kasa: Tinubu da Amaechi na rubibin wakilan doka 3,000 na APC. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Daga Tinubu har Amaechi, suna kokarin samun goyon bayan wakilan dokar jam'iyyar ne idan rade-radin yarjejeniya a jam'iyyar da ake yi bai yi aiki ba.

An tattaro yadda wakilan dokan jam'iyyar suka kai kusan 3,000 a jihohi 36 da babban birnin tarayya na kasar nan.

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

Wakilan jam'iyyar sun hada da tsoffi da kuma 'yan majalisun tarayya tare da tsoffi da kuma 'yan majalisun jihohi masu ci a yanzu.

Sunday Tribune ta binciko cewa, sune suka kai kashi daya bisa uku na jimillar wakilan da za su yanke hukunci kan makomar 'yan takarar shugabancin kasar.

Babban dakaren Amaechi an gano ya gana da tsayayyun wakilai daga kudu maso yamma sau biyu a wata daya.

Tarukan wadanda aka yi a makon gangamin jam'iyyar da ranar 5 ga watan Afirilu, an yi su ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Sakataren NSC kuma dan takarar gwamnan jihar Benue a 2019, Emmanuel Lyambee Jime, ya jagoranci wakilan Amaechi zuwa taron da kusan wakilai 100 na jam'iyyar suka halarta.

An tattaro cewa, Emmanuel ya bayyana dalilan da yasa wakilan ya dace su duba tsohon gwamnan Ribas din su bashi kuri'unsu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Wakilan da suka tattaro daga jihohi shida na kudu maso yamma, an sanar dasu cewa basu da shamaki da Amaechi matukar ya zama shugaban kasa.

Majiyar da ta halarci taron amma ta bukaci a boye sunanta, ta ce "wakilan sun sauraresu amma ba su sanar da wanda zai samu kuri'unsu ba."

A daya bangaren kuwa, Tinubu ya tattaro kusan tsayayyun wakilai 500 na jam'iyyar inda ya gana da su a otel a Abuja da yammacin ranar da aka yi gangamin taron jam'iyyar a watan da ya gabata. A yayin taron, Tinubu ya sanar da su gamsassun dalilan da ya dace ya shugabanci kasar nan.

"A yayin taron, ya sanar da mu cewa zai magance matsalar rashin tsaro da na tattalin arziki," daya daga cikin wakilan yace.

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu da sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, Opeyemi Bamidele suna daga cikin wadanda suka raka Tinubu zuwa wurin taron.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da dillalin kwayoyi a Kano dauke da sinki 250 na wiwi masu darajar N1.7m

Ribadu, wanda ya yi jawabi a taron, ya kwatanta Tinubu da dan takara mafi dacewa ga kasar nan inda ya yi kira ga wakilan da su bashi kuri'unsu.

Tsohon shugaban EFCC yace zargin rashawa da ake wa Tinubu duk na bogi ne don babu tabbaci.

Ya sanar da wakilan cewa, EFCC a karkashin jagorancinsa sun binciki Tinubu sau da yawa amma ba su samu komai na laifi tattare da shi ba.

Kafin taron Abujan, a kalla tsayayyun wakilai 200 daga jihohin kudu maso yammaci sun gana a wani otal da ke Ibadan inda suka bada tabbacin goyon bayan Tinubu.

Tawagar wakilan kudu maso yamma na samun jagorancin tsohon mataimakin gwamnan jihar Ogun kuma tsohon sanata da ya wakilci Ogun ta gabas, Sanata Gbenga Kaka da kuma tsohon sanata Legas ta yamma, Sanata Ganiyu Solomon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng