Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

  • Dr. Chris Ngige ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2023
  • Ministan kwadagon ya bayyana haka ne a lokacin da malaman jami’o'i su ka dade su na yajin-aiki
  • Wasu daliban da suka koma gida saboda an rufe jami’o’in sun fito su na yin kaca-kaca da Ministan

Abuja - Sanata Chris Ngige ya shaidawa Duniya cewa zai nemi yin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa. Ministan kwadagon kasar zai nemi tikiti ne a APC.

Jaridar Daily Trust ta ce labarin yin takarar Ministan tarayyar bai samu karbuwa sosai ba, musamman ga wadanda ke ganin Chris Ngige ya gaza a kujerarsa.

Chris Ngige ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da kungiyar ASUU ta ke yajin-aiki. ‘Daliban jami’a sun shafe tsawon makonni su na ta faman shan zaman gida.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Da mu ka bibiyi abin da makarantar mu suke fada, sai mu ka fahimci cewa mafi yawan mutane sun soki wannan lamari, musamman ganin halin da ake ciki yau.

Ra'ayin wasu masu bibiyar shafinmu

Abubakar Umar Isa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Irin wannan wai shi ne wakilin Gomnatin Buhari wajen sasanta Gomnatin da ma'aikata idon su na rikici, ashe shi yasa Daliban Jami'o'in Najeriya za suci gaba da zama a gida tsawon shekaru.”
“Allah mun gode maka, Allah kasa APC ta tsaida Shi mu student da kasa zaman gida kawai mun isheka.” – Inji Abubakar Yahaya Shika

Wani ya ke cewa “Kungiya daya an gagara shawo kan ta, to inaga rikon Najeriya.”

Kabir Tahir yake cewa:

“Wadannan mutane Allah zai yi maku hisabi. Ka da ku manta, kwanakin kididdigaggu ne. Mutane maras kirki a ko ta ina.”
Takarar APC
Chris Ngige da 'Yan APC a wajen kamfe Hoto: www.heraldngr.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

"Ministoci sun ja kaya"

Muhammad Usman Nazeef ya rubuta:

“Ministocin Buhari sunzuge kudade fa Wanan mulkin shayasa suketa Maganar takarar shugaban kasa.”

Wani Abubakar Musa Sheka, ya fito ya ce:

“Watau ko mutanen nan saboda tsabar handama da sukayi sun rasa yadda zasuyi da kudinmu, sai takara suke yi, Allah ya isa, wallahi ba mu yafe ba."

Ra’ayin Jamilu Tukur ya zo daidai da na su Nazeef da Sheka:

“Wannnan shike tabbatar Mana dacewa baqaramar sata akai a gwamnatin shugaba muhammad Buhari ba kana minister Kai tsalle Wai kanemi President.”

Abubakar Abdullahi ya tuna da wata takaddama da aka yi tsakanin Ngige ne da James Faleke, ya ce:

“Tab kana ruwa Baba Shugabanchin nigeria bana yan Victoria island boy bane na yan Mushin boy ne”

Ishaq Sanyinna yake cewa:

“Tun a nursery election zamu bajeka, Mu na ta fama da ASUU strike fiye da wata goma sha biyu.. Amma ka kasa shawo kan matsalar, harma kake wannan gur6ataccen tunanin tsayawa takara.”

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Ngige zai yi takara

Shi dai Sanata Chris Ngige wanda tun 2015 yake rike da kujerar Ministan Kwadago ya bayyana cewa zai kaddamar da takarar shugaban kasarsa a gobe Talata.

Tsohon Gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa ya yanke shawarar kaddamar da takarar ne bayan Ubangiji ya masa magana a lokacin da ye ke ibadarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel