2023: Ubangiji Ya Min Wahayi, Zan Ƙaddamar Da Takarar Shugaban Ƙasa Ta Ranar Talata, Ministan Buhari

2023: Ubangiji Ya Min Wahayi, Zan Ƙaddamar Da Takarar Shugaban Ƙasa Ta Ranar Talata, Ministan Buhari

  • Sanata Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka, ya bayyana cewa zai kaddamar da takarar shugaban kasarsa ranar Talata
  • Ngige ya bayyana cewa ya yanke shawarar kaddamar da takarar ne bayan Ubangiji ya masa magana a lokacin da ye ke ibada na lent
  • Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya sanarwa magoya bayansa cewa ba su zai kunyata su ba idan aka bashi damar zama shugaban kasa

Ministan Kwadago da Ayyuka, Sanata Chris Ngige, ya ce Ubangiji ya masa magana game da niyyarsa na takarar shugaban kasa kuma zai kaddamar da takarar ranar Talata.

Daily Trust ta rahoto cewa Ngige ya furta hakan ne a ranar Asabar da yamma a lokaci da mambobin jam'iyyar APC suka tarbe shi a wani mahada tsakanin Jihar Anambra da Enugu.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Lokacin Da Zai Ƙaddamar Da Takararsa Na Shugabancin Ƙasa

2023: Ubangiji Ya Min Wahayi, Zan Ƙaddamar Da Takarar Shugaban Ƙasa Ta Ranar Talata, Ministan Buhari
2023: Ubangiji Ya Min Wahayi, Zan Yi Takarar Shugaban Ƙasa, Ministan Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Da ya ke yi wa dandazon mutanen jawabi, wanda tunda farko suka bukaci ya fito takarar, Ngige ya ce ya tuntubi mutane, kuma ya yi addu'a sannan Ubangiji ya amsa shi.

"Ina son in tabbatar muku lokacin 'azumin lent' ta kare daren jiya, kuma a lokacin, mun kusanci Ubangiji. Mun yi addu'o'i da azumi. Munyi magana da Ubangiji da mala'ikunsa kuma Ubangiji ya mana magana. Ubangiji ya min magana. Ina son tabbatarwa mutane ba zan basu kunya ba. Zan muku magana a irin harshen da kuke fahimta," in ji shi.

A daina kwatanta ni da Peter Obi da Willie Obiano, wata 34 kadai na yi, Ngige

A cewarsa, a matsayinsa na gwamnan Jihar Anambra cikin watanni 34, ya yi ayyukan da wasu ba su iya yi ba cikin shekaru takwas a ofis.

Kara karanta wannan

Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

Amiloaded ta rahoto cewa Ngige ya kara da cewa zai maimaita irin wadannan ayyukan a kasa, idan an bashi dama.

Ya ce babban kuskure ne mutane su kwatanta shi da Peter Obi da Willie Obiano, yana mai cewa cikin wata 34 ya fi su ayyuka.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel