Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

  • Malamin addinin kirista ya bayyana cewa, matsalar Najeriya ba za ta kau ba sai an samu mai tsoron Allah
  • Bai kamata a samu shugabannin da basu amsa kiran ubangiji ba, inji faston Deeper Life Kumuyi
  • Ya bayyana haka ne yayin da ya kai wata ziyarar ibada zuwa jihar Ribas a yankin kudancin Najeriya

Jihar Ribas - Gabanin zaben 2023, babban malamin Deeper Life Christian Life, Fasto William Kumuyi, ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah a wannan lokacin domin su canza fasalinta, inji rahoton Punch.

Kumuyi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Fatakwal, jim kadan bayan isowarsa babban birnin jihar Ribas domin gudanar da wani shirin addinin kirista mai suna ‘Power for the Present Hour crusade’.

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Fasto Kumuyi ya fadi irin shugabannin da ya kamata a samu
Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya samu tarba a filin jirgin sama daga ’yan coci, ’yan agaji, daliban makarantar sakandare ta Deeper Life, da kuma ‘yan kungiyar Pentecostal Fellowship ta Nigeria.

Da aka tambaye shi ko ya dace kiristoci su shiga siyasa, malamin ya ce ba tare da la’akari da addini ba, masu tsoron Allah ne ya kamata su rika jagorantar al'umma.

A kalamansa:

“Ba Kiristoci kadai ba, duk wanda Allah ya kira ko Kirista ne ko Musulmi ne ko kuma duk wanda Allah ya kira, ya kamata su amsa kiran Allah, domin kasarmu ta ci gaba.”

Kumuyi ya kuma bayyana cewa, taron na Fatakwal da za a fara daga ranar Alhamis, 14 ga Afrilu zuwa 18 ga Afrilu, 2022, zai kasance mai cike da wa'azantarwa da haske, mai taken ‘Come and Receive Power for the Present Hour.’

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Hakazalika, ya kuma yi addu'ar neman sa'a daga ubangiji a wannan taro da za su yi. A bangare guda ya yiwa kasa addu'ar daidaito, kamar yadda Independent ta tattaro.

Shima da yake jawabi, shugaban kungiyar PFN reshen jihar Ribas, Rev Minaibi Dagogo-Jack, ya bayyana cewa yana da kyau kiristoci su shiga harkar siyasa domin jama’a za su yi murna ne kawai idan adalai suka yi mulki.

Yayin da ake ta cece-kuce kan man fetur, majalisa ta amince da bukatar Buhari na kashe N4tr a tallafin mai

A wani labarin, majalisun dokokin kasar nan sun amince da bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bijiro da ita na ware naira tiriliyan 4 na kudin tallafin man fetur, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Majalisar dattawa da ta 'yan majalisu sun amince da bukatar shugaban kasar ne bayan sun yi la’akari da rahotannin kwamitocinsu kan harkokin kudi.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya bai wa wadanda masallaci ya murkushe kyautar N5m a Yobe

Amincewar ta biyo bayan bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na sake fasalin kasafin kudin shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel