Sakataren Fadar Gwamnatin Jihar Ebonyi Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Shiga Takara a 2023

Sakataren Fadar Gwamnatin Jihar Ebonyi Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Shiga Takara a 2023

  • Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Kenneth Ugbala, ya yi murabus daga mukaminsa kuma ya shiga tseren takara
  • Mista Ugbala ya tabbatar da aniyarsa a Sakatariyar APC ta jiha jim kadan bayan gana wa da kwamitin gudanarwa na jam'iyya
  • Ya ce ya gana da shugabannin jam'iyya mai mulki ne domin neman shawari da goyon bayan su

Ebonyi - Sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Kenneth Ugbala, ya yi murabus daga kan kujerarsa domin maida hankali wajen cika burinsa na zama Sanata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Mista Ugbala ya bayyana haka ga manema labarai bayan wani taron sirri da mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi a Sakatariyar jam'iyya dake Abakaliki.

Taswirar jihar Ebonyi.
Sakataren Fadar Gwamnatin Jihar Ebonyi Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa, Ya Shiga Takara a 2023 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tsohon sakataren gwamnatin na hangen kujerar Sanata mai wakiltar mazaɓar Ebonyi ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala ta kunno kai a APC, Wani Babban jigo ya fice daga jam'iyyar, ya koma PDP

Daily Trust ta rahoto a jawabinsa ya ce:

"Na zo na yi shawara da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar mu domin samun amincewa da goyon baya game da aniyarmu ta neman Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya a zaɓen 2023."
"Kun sani cewa ta jam'iyyar siyasa zaka bi har ka samu ɗarewa kan mulki, kuma kafin taka wani mataki wajibi ka nemi shawarin shugabannin jam'iyya, kuma ka nemi amincewar su, shiyasa na zo nan."

SSG ya tabbatar da aje aiki

Game da murabus ɗinsa, Mista Ugbala, ya ce yana da cikakken masaniya game da sabon kundin dokokin zaɓe, kuma ya bi duk wasu matakai na biyayya, wanda ya haɗa da murabus daga kujerarsa.

"Na san tanadin kundin zaɓe kuma doka na da ƙarfi. Lokacin da aka naɗa ni da kuma yanzu da na zo nan, duk na bi matakan da ya dace. Kuma ina da Uban gida, shi ne zai nuna mun abin da yake wajibi."

Kara karanta wannan

2023: ‘Dan takarar APC ya musanya rade-radin hakura da neman zama Shugaban kasa

"Ni ba irin mutanen da zasu bayyana takardar Murabus ɗin su a fili bane na kaita wurin da ya dace."

A wani labarin kuma Abinda shugaba Buhari ya faɗa wa Gwamnan APC bayan sanar da shi aniyarsa ta takara a 2023

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takara a 2023.

Wata majiya ta bayyana cewa shugbaan ya ƙarfafa wa gwamnan guiwa ya cigaba da kokarin cika burinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel