'Yan Jam'iyyar PDP Fiye Da 1,500 Sun Ɗunguma Sun Koma APC a Wata Jihar Arewa

'Yan Jam'iyyar PDP Fiye Da 1,500 Sun Ɗunguma Sun Koma APC a Wata Jihar Arewa

  • Fiye da mutane 1,502 ‘yan jam’iyyar PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a gundumar Pil Ganu da ke karamar hukumar Langtang ta arewa a Jihar Filato
  • -Shugaban karamar hukumar, Barista Zulfa Rimven ne ya amshe su inda jagoran sauya shekar, Ringa Nanlok ya ce sun gamsu da mulkin jam’iyyar
  • Shugaban karamar hukumar ya samu rakiyar kwamishinan gidaje, Hon Brian Bintim Dadi da sauran ‘yan takaran APC na 2023 inda ya ce za a tabbatar musu da adalci

Filato - Jam’iyyar APC ta samu karuwar fiye da mambobi 1,502 wadanda suka bar jam’iyyar PDP a gundumar Pil Gani da ke karamar hukumar Langtang ta arewa a Jihar Filato, The Nation ta rahoto.

Barista Zulfa Rimven, shugaban karamar hukumar Langtang ta arewa ne ya amshe su.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar APC, ya koma PDP

'Yan Jam'iyyar PDP Fiye Da 1,500 Sun Ɗunguma Sun Koma APC a Wata Jihar Arewa
'Yan Jam'iyyar PDP Fiye Da 1,500 Sun Koma APC a Filato. Hoto: The Nation.
Asali: Twitter

Jagoran masu sauya shekar, Ringa Nanlok ya ce sun gamsu da shugabancin karamar hukumar da kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong.

Shugaban karamar hukumar ya ce shigarsu jam’iyyar nasara ce babba

ICIR ta ruwaito yadda Rimven ya hada kwamiti ta musamman don amsar sabbin ‘yan jam’iyyar.

Shugaban karamar hukumar ya samu rakiyar Kwamishinan gidaje, Hon. Brian Bintim Dadi da kuma sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC na zaben 2023, kuma ya tabbatar wa da wadanda suka sauya shekarar cewa zai yi musu adalci.

Shugaban karamar hukumar, wanda ya kwatanta lamarin a matsayin girbar fiye da mambobi 1,502, sannan ya nuna farin cikinsa akan sabbin mambobin wadanda yawancinsu tsofaffin shugabanni ne da kuma masu matsayi a jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC Ya Faɗa Wa Ƴan Najeriya Irin Ƴan Siyasan Da Ya Kamata Su Ƙaurace Wa

Ya bukaci su yi amfani da mutanensu wurin tabbatar da samun nasarori ga jam’iyyar a zaben 2023.

Ya nemi sabbin ‘yan jam’iyyar da su kasance masu aiki tukuru wurin kawo ci gaban APC

Ya yi kira ga sabbin da tsofaffin mambobin jam’iyya mai mulki akan su yi aiki tukuru wurin samar da zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na gundumar, Mr Vongdul ya tabbatar wa sabbin mambobin jam’iyyar APC din cewa dawowarsu jam’iyyar nasara ce mai yawa da shugaban karamar hukumar ya yi.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Kara karanta wannan

Babban magana: Dubban 'yan APC da PDP a Katsina sun koma jam'iyyar su Kwankwaso NNPP

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel