Buhari Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Yana Ta Cika Wa 'Yan Najeriya Alƙawuran Da Ya Ɗauka Yayin Kamfen Ɗin Zaɓen 2015

Buhari Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Yana Ta Cika Wa 'Yan Najeriya Alƙawuran Da Ya Ɗauka Yayin Kamfen Ɗin Zaɓen 2015

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya tsaya akan batun cewa ya cika duk alkawuran canjin da ya yi wa ‘yan Najeriya yayin kamfen din zaben 2015
  • Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ya ce cikin abubuwan canjin da ya yi wa ‘yan Najeriya alkawari shi ne samar da muhalli kuma ya cika
  • A cewarsa, ba lallai ne su samu damar ganawa da ko wanne dan Najeriya ba, amma bunkasa tattalin arziki da ababen more rayuwar da suka samar sun riski kowa

Edo - A ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda gwamnatinsa ke cika duk alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya yayin kamfen din zaben 2015, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau

Ya ce ya samar da ci gaba ta hanyar muhalli, wanda hakan daya daga cikin hanyar bunkasa ababen more rayuwar kasa ne. A cewarsa mulkinsa ya yi matukar kawo ci gaba a harkar gidaje kamar yadda ya dauki alkawari a 2015.

Buhari Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Yana Ta Cika Wa Yan Najeriya Alƙawuran Da Ya Dauƙa a Kamfen Ɗin 2015
Shugaba Buhari Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Yana Ta Cika Wa Yan Najeriya Alƙawuran Da Ya Dauƙa a Kamfen Ɗin 2015. Hoto: Fadar Shugaban Kasa.
Asali: Depositphotos

Shugaban kasa ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar da shirin gidaje na 68-unit wanda Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya ta yi karkashin shirin Gidajen Tarayya (NHP), Phase One da aka yi a kan titin Benin-Auchi a Benin, Jihar Edo.

Buhari ya ce a hankali romon demokradiyya zai riski kowa

Buhari wanda ya samu wakilcin Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya kada baki ya ce:

“Lokacin da jam’iyyarmu take yi muku kamfen a 2015, cikin abubuwan da muka yi muku alkawari shi ne canji. Kuma wadannan gine-ginen suna cikin cika alkawuran da muka dauka na canji.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

“Wannan misali ne na wasu hanyoyin kawo ci gaba da gwamnati take yi kuma ina mai tabbatar muku da cewa idan filaye suka samu, Gwamnatin Tarayya za ta yi fiye da haka.
“Ba lallai mu gamu da ko wanne dan Najeriya ba, amma tabbas bunkasar tattalin arziki da samar da kayan more rayuwar da muke yi kamar shirin Gidaje na Tarayya da sauransu za su riski kowa.”

An bai wa tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa kyautar biyu daga cikin gidajen

Nigerian Tribune ta rahoto cewa Shugaban kasa ya ce an yi kaddamarwar ne a matsayin cika alkawarin da aka daukar wa ‘yan kungiyar wasan kwallo kafa ta Super Eagles, bayan sun lashe gasar kwallon Afirka ta 1994 da Wilfred Agbonavbare da kuma Marigayi Thompson Oliha, wanda ya samu wakilcin matarsa, Iris, wadanda aka ba ko wannensu gida mai uku.

Ya kula da cewa a jihar da aka kammala gina gidajen, gwamnati ta bayar da kwangilar kulawa da gidajen ga wasu masu kananun sana’o’i don tabbatar da cewa an ci gaba da kula da gidajen da kyau, kuma hakan salon samar da aiki ne ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnati da mutanen Jihar Edo akan kokarinsu wurin tabbatarwa da kuma kaddamar da gidajen, wanda hakan zai taimaka wurin kawo walwalar mutanen jihar.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel