Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

  • Joe Igbokwe ya yi kira na musamman ga wadanda suke shirin yin takara a jam’iyyar APC mai mulki
  • A cewar Igbokwe, muddin Asiwaju Tinubu ya kawo mutum cikin siyasa, bai dace ya yi takara da shi ba
  • Mai ba gwamnan na jihar Legas shawara ya na so Gwamnoni su goyi bayan takarar ubangidansa

Lagos - Daya daga cikin jagororin APC a jihar Legas, Joe Igbokwe ya bukaci duk wasu masu neman mulki da Bola Tinubu ya kafa su a siyasa, su hakura.

Tun ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu 2022, Joe Igbokwe ya ke ta maganganu a shafin Facebook, bayan jin cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai nemi tikitin APC.

Da yake bayani a shafinsa, Igbokwe ya yi kira ga masu harin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC, su yi biyayya ga wanda ya fara kawo su harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

"Bari in fada a nan saboda tarihi ya rubuta. Idan ka na cikin wadanda Asiwaju ya kawo ka (siyasa), kuma ka kwallafa rai a kujerar shugaban kasar Najeriya…
…To ka ba shi girma, ka janye daga wannan takarar.”

Amma mutane ba su kyale hadimin gwamnan na jihar Legas haka ba, sun yi ta maida masa martani.

Osinbajo, Ambode, Fashola da Sanwo Olu
Tsofaffin yaran Tinubu a siyasa Hoto: @joeigbokwe.igbokwe
Asali: Facebook

Martanin da jama'a su ke yi masa

Emeka Nwokeocha ya ce

“Najeriya ta fi karfin wani mutum daya. Duk wanda yake ganin ya isa ya rike kujerar shugaban kasa, ya fito takara. Ba na son wannan siyasar ta ubangida. Shirmen banza. Abin kunya ne.”
“Ina tunani tauraruwar Asiwaju a siyasa ta dushe idan ya na jin tsoron gwabzawa da tsofaffin yaransa a zabe.”

- Sola Fasure

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

“Kowane uba ya na da yaron da ya fi shi. Idan uba ya ce dole sai ya fi duka ‘ya ‘yansa, wannan ba uban kwarai ba ne. A duba dai ‘danuwa.”

- Igwe Chukwuka Igwe

A ra’ayin O. Tobi Martins, babu dalilin da za a janyewa Tinubu, a fito ayi zaben fitar da gwani, domin ya na sa ran tsohon gwamnan ne zai samu tutan jam’iyya.

Can kuma tsohon kakakin na APC ya rubuta cewa Bola Tinubu ba karamin ‘dan siyasa ba ne, don haka duka gwamnoni su mara masa baya a zaben fitar da gwani.

A wata maganar kuma ya nuna cin amana ne wadanda Tinubu ya kawo, su yi takara da shi.

APC ta caccaki Osinbajo

Dazu aka ji cewa mai magana da bakin jam’iyyar APC a Legas ya yi wa Yemi Osinbajo kaca-kaca ganin ya yarda ya goge raini da Bola Tinubu a zaben fitar da gwani.

Kakakin APC na jihar Legas, Seye Oladejo ya ce a filin zaben tsaida 'dan takara, za a ga abin da Farfesa Yemi Osinbajo zai tabuka domin bai da kowa a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Dokubo Asari ya caccaki Gwamnan PDP, ya ce takararsa a 2023 ba za ta kai labari ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel