2023: Ministan Buhari Ya Shiga Jerin Masu Takarar Gwamna a Jiharsa

2023: Ministan Buhari Ya Shiga Jerin Masu Takarar Gwamna a Jiharsa

  • Dr Uche Sampson Ogah, Karamin Ministan Ma'adinai da Cigaban Karafa ya shiga jerin yan takarar gwamna a Abia
  • Ogah ya ayyana shigarsa takarar ne a gidansa da ke kauyensu na Onuaku Uturu, Karamar Hukumar Isiukwato a Jihar Abia
  • A yayin taron da aka yi, an kaddamar da shugabannin wata kungiya ta yakin neman zabe mai suna Abia Rejoice

Jihar Abia - Karamin Ministan Ma'adinai da Cigaban Karafa, Dr Uche Sampson Ogah, ya sanar da cewa zai yi takarar gwamna a babban zaben 2023 da ke tafe.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ministan ya sanar da takarsa ne yayin da ya ke ganawa da mutanen garinsu a Onuaku Uturu, Karamar Hukumar Isiukwato a Jihar Abia.

2023: Ministan Buhari Ya Shiga Jerin Masu Takarar Gwamna a Jiharsa
2023: Ministan Ya Shiga Takarar Gwamna a Jiharsa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Easter Na 2022

Mutane daga kauyuka 42 suka iso gidan Ogah don yin kira gare shi ya yi takara

Ogah ya ce mutanen garinsu daga kauyuka 42 sun hadu a gidansu sun bukaci ya fito takarar kamar yadda today ta rahoto.

Wani na hannun daman ministan, Fasto Eugene Chuwa, ya bayyana niyarsa na yin takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan Isuikwuato a karkashin jam'iyyar APC.

Abin da ya fi daukan hankali a wurin taron shine kaddamar da shugbannin Abia Rejoice, wata kungiya ta yakin neman zabe.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Ya Zama Dole a Bar Kudu Maso Gabas Ta Mulki Najeriya a 2023

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel