2023: Jerin jihohi 8 da PDP ka iya shan kaye idan har ta baiwa dan arewa tikitin shugaban kasa

2023: Jerin jihohi 8 da PDP ka iya shan kaye idan har ta baiwa dan arewa tikitin shugaban kasa

Gabannin babban zaben 2023, ana ta rade-radin cewa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta baiwa dukkanin yankunan kasar damar shiga tseren neman tikitinta na shugaban kasa.

Sai dai kuma, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue wanda shine shugaban kwamitin tsarin karba-karba na PDP ya yi watsi da ikirarin da wasu majiyoyi suka yi.

Ya ce kwamitin karba-karban ya yanke hukunci kan lamarin amma kwamitin NEC bai riga ya tabbatar da shi ba.

2023: Jerin jihohi 8 da PDP ka iya shan kaye idan har ta baiwa dan arewa tikitin shugaban kasa
2023: Jerin jihohi 8 da PDP ka iya shan kaye idan har ta baiwa dan arewa tikitin shugaban kasa Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Yayin da ake tsaka da batun, jaridar ThisDay ta hango abun da ka iya faruwa da PDP a zaben 2023 idan har ta bude tikitinta sannan wani dan takara daga arewa ya yi nasarar lashe zaben fidda gwaninta.

A cewar jaridar, jam’iyyar adawar na iya shan kaye a wasu manyan jihohin kudu idan ta tsayar da dan arewa a matsayin dan takararta. Hakan zai saba kiraye-kirayen da kudu ke yi na a bari yankin ya samar da magajin shugaban kasa Buhari a 2023.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Rahoton ya lissafo jerin jihohin da PDP ka iya rasawa a zaben 2023 idan ta yi biris da kiraye-kirayen da kudu ke yi sannan ta tsayar da dan arewa.

Ga jerin jihohin:

1. Oyo

2. Delta

3. Rivers

4. Abia

5. Enugu

6. Akwa Ibom

7. Benue

8. Cross River (koda dai APC ce ke rike da madafun iko a yanzu haka, PDP na da karfi a jihar)

Rahoton ya bayyana cewa gabatar da dan takara daga arewa baya nufin PDP za ta yi karfi a manyan jihohin arewa domin cike gurbin da za ta iya rasawa a kudu.

Gwamna Masari ya ayyana gobe Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin hutu, ya bayyana dalili

Kara karanta wannan

Masu fasa bututu sun taso Najeriya a gaba, ana asarar Naira Biliyan 600 a kowace rana

A wani labarin, mun ji cewa Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana Litinin, 11 ga watan Afrilu, a matsayin ranar hutun aiki.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar da wannan hutun ne domin ma’aikata da iyalansu su samu damar kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da za a gudanar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Isyaku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel