Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban ƙasa zai ayyana shiga takarar gaje Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban ƙasa zai ayyana shiga takarar gaje Buhari a 2023

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai bayyana shiga takarar shugaban ƙasa nan da 'yan kwanaki masu zuwa
  • Wata majiya mai ƙarfi a fadar Aso Villa ta ce an kammala duk wasu shirye-shirye da ya kamata
  • An jima ana raɗe-raɗin cewa Osinbajo na son ɗorawa daga inda Buhari zai tsaya amma hadimansa na musantawa

Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a wasu ƴan kwanaki masu zuwa zai ayyana shiga tseren takarar shugaban ƙasa a hukumance ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Tribune Online ta tattaro cewa hakan na zuwa ne bayan jita-jita ta yawaita da kuma musanta lamarin da hadimansa da abokanansa suka yi.

An jima ana yaɗa jita-jitar cewa Mataimakin shugaban zai nemi takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban ƙasa zai ayyana shiga takarar gaje Buhari a 2023 Hoto: Professor Yemi Osinbajo/Facebook
Asali: Facebook

A baya an yaɗa cewa Farfesa Osinbajo zai fito da kudirin dake zuciyarsa na takara a ranar 7 ga watan Afrilu , amma kuma hakan ba ta faru ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana abinda zata yi don ceto Fasinjojin Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Me ya tabbatar da rahoton a yanzu?

A halin yanzu, wata majiya a cikin fadar shugaban ƙasa, ranar Alhamis (Jiya), ta ambato cewa shiri ya kammala domin ayyana shiga takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Majiyar daga Aso Rock ta yi wannan jawabi ne bisa sharaɗin ɓoye bayananta, inda ta ce, "Zai bayyana shiga tseren cikin yan kwanaki ƙalilan masu zuwa."

Tuni dai ƙungiyoyin dake goyon bayan mataimakin shugaban suka tsara Fastoci, suka manna su a wurare daban-daban na gwamnati a babban birnin tarayya Abuja.

Wasu daga cikin hadiman Osinbajo da aka tuntuɓa domin su bayyana ainihin ranar da Osinbajo zai bayyana shiga takara, sun ƙi yin hakan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shin Osinbajo zai fafata da Tinubu?

Kara karanta wannan

2023: Ba zan janye ba, waya sani ko yan Najeriya ni suke mutuwar son na gaji Buhari, Ɗan takara a PDP

Wasu rahotanni da ake yaɗawa na nuna cewa Osinbajo ya ɗau alƙawarin ba zai nemi takara ba matukar jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, na neman Ofishin.

Tsohon gwamnan Legas ɗin ya bayyana cewa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na neman kujera lamba ɗaya, duk da yace wannan ne babban burin rayuwarsa.

A wani labarin kuma Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai mai daɗi

Matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta tabbatar da shiga jam'iyyar SDP domin cika burinta.

Khadijat ta ayyana shiga tseren gaje kujerar shugaban ƙasa buhari a zaɓen 2023 amma ba ta shiga jam'iyya ba sai yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel