Gwamnatin Buhari ta bayyana abinda zata yi don ceto Fasinjojin Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Gwamnatin Buhari ta bayyana abinda zata yi don ceto Fasinjojin Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

  • Gwamnatin tarayyan Najeriya ta tabbatar da cewa sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen ceto mutane da yan ta'adda suka sace a Jirgin ƙasa
  • Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don samun nasara
  • Ya ƙara da cewa ma'aikatarsa ta cimma dukkan abinda ta sa a gaba a shekarar 2021 da kwatan farko na 2022

Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa iyalan Fasinjojin jirgin ƙasa da yan ta'adda ke rike da su cewa zata yi duk me yuwuwa wajen ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, shi ya baiwa iyalan wannan tabbaci a wurin taron manema labarai na ministoci da aka saba shiryawa a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

A makon da ya gabata ne, wasu yan ta'adda suka farmaki Jirgin ƙasa dake aiki a tsakanin Abuja-Kaduna, inda suka kashe mutum 8, suka yi garkuwa da adadi mai yawa na fasinjoji.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Gwamnatin Buhari ta bayyana abinda zata yi don ceto Fasinjojin Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Amaechi, wanda ya samu wakilcin ƙaramin ministan Sufuri, Gbemisola Saraki yace ma'aikatarsa na cigaba da tuntubar hukumomin tsaro akai-akai kan ceto mutanen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ya kara da cewa ba zai yuwu ya ba da cikakken bayanin shirin da suke yi da hukumomin tsaro ba domin gudun dawo da hannun riga baya da kuma tsaro.

Wasu iyalan da lamarin ya shafa sun je har wurin taron domin nuna fushin su kan gaza ceto yan uwansu da gwamnatin ta yi na tsawon kwanaki 12.

Wane nasarori ma'aikatar Sufuri ta samu?

Da yake jawabi kan nasarorin da ma'aikatarsa ta samu a shekarar 2021 da kwatan farko na 2022, Ministan ya ce mafi yawan manufofin da ma'aikatar ta sa a gaba ta yi nasarar kammala su.

Kara karanta wannan

Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje

Yace ma'aikatar Sufuri ta yi nasarar inganta tsaro a zirga-zirgar ruwa, inda ya ƙara da cewa Najeriya ta fice daga jerin ƙasashen da yan fashin ruwa suka addaba.

Bugu da ƙari, Mista Amaechi, yace tuni kudirin kafa hukumar Sufuri (NTC) ya kai teburin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, domin zartarwa.

"Hakan zai sa majalisar kula da sufurin ruwa ta ƙasa ta koma hukumar NTC," inji Ministan.

A wani labarin na daban kuma Yayin da Jam'iyyar APC ke ganin ta shirya tunkarar 2023, Ɗan majalisa ya fice daga jam'iyyar

Ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Cater Dike-Umeh, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa APGA.

Ya ce ya sake dawowa APGA da take gida a gare shi saboda ba shi da dalili da zai kafa na barinta watanni Bakwai da suka shuɗe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel