Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

  • Matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta tabbatar da shiga jam'iyyar SDP domin cika burinta
  • Khadijat ta ayyana shiga tseren gaje kujerar shugaban ƙasa buhari a zaɓen 2023 amma ba ta shiga jam'iyya ba sai yanzu
  • Ta ce SDP ce ta yi dai-dai da kyawawan manufofin da take tattare da su, kuma lokaci ya yi da za'a samu sabon zubi a Najeriya

Yar takarar shugabancin Najeriya, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana cewa ta rungumi jam'iyyar SDP ne saboda ita ce ta matasa da kuma mata.

Khadihat ta yi wannan jawabin ne ranar Alhamis yayin da take sanar da matakin komawa jam'iyyar SDP, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Da take jawabi, yar takarar wacce ba ta wuce shekara 38 ba a duniya, ta ce ta rungumi SDP ne saboda ta yi dai-dai da kudirinta da manufarta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Sha Kaye a Kotu, An Ƙi Ƙwace Kujerar Gwamna Ayade Da Ya Koma Jam'iyyar APC

Yar takarar shugaban ƙasa, Khadijah Okunnu-Lamidi.
Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Najeirya na bukatar sabon zubin tawagar zaƙaƙurai, jarumai na gaske waɗan da ba su bukatar komai da ya wuce su sauke nauyin dake kansu, kuma ba su bukatar ko sisi da sunan siyar da martabar mutanen mu."
"Muna tsaye anan ne don mu ayyana cewa har yau muna da yaƙini kan Najeriya. Wannan ɗalilin ne mace da ba kowa ba wacce ta yi imani da tsarin matasa, nake sanar da shiga SDP a hukumance."
"Zamu iya cewa jam'iyyar mu zata tsaya tsayin daka ta tabbatar da ingantaccen ilimi, da kuma isassun wuraren kiwon lafiya. Jam'iyya ce dake ba matasa dama kuma ina farin cikin zama ɗaya daga ciki."

Meyasa ta zaɓi shiga SDP?

Misis Khadijat ta faɗi cewa ta zaɓi SDP a kan sauran jam'iyyun siyasa ne saboda ita kaɗai ta zo layi ɗaya da hangenta da kuma burinta.

Kara karanta wannan

2023: Ba zan janye ba, waya sani ko yan Najeriya ni suke mutuwar son na gaji Buhari, Ɗan takara a PDP

"Na zaɓi shiga SDP ne saboda ta yi alƙawarin aiki da ni. Na yi imanin cewa za'a sha burtu dani har na samu nasara, idan ban tsallake zaɓen fidda gwani ba, ba maganar babban zaɓe."

A wani labarin kuma Shugaban ma'aikatan fadar gwamna da Kwamishinoni 9 sun yi murabus daga mukamansu

Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Delta, Ovie Agas, ya yi murabus daga kan kujerarsa kuma ba takara zai yi ba a 2023.

Kwamishinan yaɗa labarai, Mista Aniagwu, ya ce sauran kwamishinoni 9 da hadimai sun yi haka ne saboda shiga takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel